Hanyoyin da za ku kauce wa fadawa hannun masu zambar fili

Asalin hoton, Others
Tun bayan sa-in-sa da aka samu tsakanin ministan Abuja, Nyesom Wike da laftanar AM Yerima kan fili, ƴan Najeriya ke ta tattauna irin matsalolin da batun fili ke haifarwa.
Rigimar fili na ɗaya daga cikin abubuwan da ke addabar birane ciki har da Abuja babban birnin Najeriya.
Hakan ne ya sa BBC ta yi nazari dangane da salo daban-daban na rikicin filaye da kuma hanyoyin da za a bi domin ƙwatar ƴancinku.
Mece ce rigimar fili?
A manyan birane ana samun yanayin da mutum biyu ko uku koma fiye da hakan da sunansu ke kan takardun mallakar fili daya.
"Abin da suke yi shi ne ko dai filin naka ne na asali sai wani ya zo ya sayar wa da wasu. Ko kuma kai ma ka sayi filin da ke ɗauke da sunayen wasu. Ko kuma wani kawai zai zo filinka ya fara gini saboda ya ba shi sha'awa."
"Kuma daga ƙarshe ba yadda za ka yi sai dai a ba ka wani filin ko kuma kuɗinsa. Shi ya sa wasu da zarar sun ga an fara gini a filinsu sai su gayyato ƴan daba su rushe shi," in ji Salisu Ali, wani mai harkar filaye da gidaje a Abuja da Kano.
Laifin waye?
Salisu Ali ya yi ƙarin haske cewa duk da cewa masu ƙwacen fili su ne da laifi kuma ya kamata a rinƙa hukunta su amma hukumomin da ke kula da filaye a jihohi da babban birnin tarayya sun fi laifi.
"Misali, idan za ka sayi fili ya kamata ka je hukumomin da ke ɗauke da bayanan filayen, to a nan ana samun wasu ma'aikata ɓata-gari da ke sauya takardu ko kuma su ƙara sunan wani a kan sunan asali da ke kan fili. Ka ga sun janyo faɗa.
"Kuma abin mamaki idan dukan ku kuka je neman tattancewa sai ku ga dukan ku kuna da mallaka a filin. To wannan laifin hukumomin ne."
Abin da ya kamata ku yi
Malam Salisu Ali ya ce ana samun yanayin da wasu masu fili ke haƙura su bar wa Allah saboda ba za su iya rigimar ƙwatar fili ba.
"Wasu su sana'arsu kenan rigimar fili. Za su iya kashe kuɗaɗe da lokaci masu yawan wajen shari'a. Wasu kuma sai su ce sun bar wa Allah. Wasu kuma za su karɓi wani filin daban da wataƙila bai kai nasu daraja."
Sai dai kuma masanin harkar filin da gidaje ya lissafa wasu hanyoyi guda biyar na ƙwatar ƴanci da gujewa fadawa rigimar fili.
- Tantance sahihancin takardun fili: Kafin mutum ya nemi haƙkinsa dangane da filin da ake rigima a kansa, to abu na farko shi ne ya tabbatar cewa shi ne mamallakin filin na asali ta hanyar tattara dukkannin takardun filin kamar takardun saye, rasit da duk wasu takardu da suka jiɓanci cinikin.
- Sanar da shugabannin yanki: A duk lokacin da ka wayi gari ka ga wani ya fara ci maka iyaka ko kuma ya fara gini a filinka, to abu na biyu da za ka yi shi ne ka kai ƙorafi a rubuce ga hukumomin yankin domin kafa hujja.
- Tuntuɓar lauyoyi: Abu na gaba kuma shi ne ka tuntuɓi ƙwararrun lauyoyi waɗnda suka ƙware a harkokin ƙasa da kadara domin su ne za su ba ku shawara kan yadda za ku shigar da ƙara.
- Ƙulla alaƙa da maƙwabta: Yana da kyau mai fili ya zama yana da alaƙa mai kyau da maƙwabtan filin nasa saboda ɓacin rana. Maƙwabtanka sun san wane ne asalin mai wurin. Idan kana da alƙa da su akan samu lokacin da suke sanar da kai idan wani zai ci maka iyaka.
- Sanin ƴancin kai: Rashin sanin ƴancin da mutum yake da shi a matsayinsa na mai fili ko gida yana taimakawa wajen sarayar da ƴancin. Idan mutum ya san ƴancin da tsarin mulki ya ba shi to komai zai zo da sauƙi a lokacin fafutukar ƙwatar filin.
Illoli uku na rigimar fili
Rigimar fili tana taka babbar rawa wajen abubuwa guda uku:
- Ɗaiɗaita iyali: Wataƙila iyalai sun haɗa ƴan kuɗadensu sun sayi fili da manufar ginawa amma sakamakon ƙwace filin nasu sai iyalan su ɗaiɗaita. "Idan a gidan haya suke za a iya korar su," in ji Salisu Ali.
- Tsiyata al'umma: Sakamakon irin yawan kuɗaden da jama'a ke sakawa wajen sayen filaye, idan aka samu rigimar da ta kai ga cinye musu filin to iyalan kan fada yanayin talauci mai dogon zango.
- Illata ƙasar noma da bishiyoyi: Sakamakon buƙatar da jama'a ke da ita kan filaye saboda yadda suke samar da kuɗaɗe, hakan kan haifar da cinye gonaki da wuraren damshi domin gine-gine wanda ke illata ƙasar noma da bishiyoyi.









