Man Utd za ta sayar da Maguire, Haaland ba zai koma PSG ba

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta saurari tayi waɗansu ƙungiyoyi domin sayar da ƙan ƙwallon Ingila, Harry Maguire a watan Junairu. (Jaridar Star).
Ɗan wasan gaba na Norway Erling Haaland, mai shekaru 24 ya yanke shawarar ci gaba da kasancewa a Manchester City kuma bai da sha'awar koma wa Paris St-Germain. (Jaridar El Nacional).
Manchester City na son sayen golan ƙasar Portugal mai shekaru 25, Diogo Costa daga ƙungiyar Porto, a matsayin wanda zai maye gurbin ɗan Brazil Ederson,(Jaridar Football Insider).
Real Madrid da Barcelona na son ɗan ƙwallon Sifaniya mai shekaru 21 wanda a yanzu yake murza leda a Benfica, Alvaro Fernandez Carreras. (Jaridar O Jogo).
Ita ma Liverpool na ƙoƙarin ganin ta saye ɗan ƙwallon na Benfica. (Jaridar AS).
Chelsea da Tottenham da kuma Liverpool na sa ido a kan ɗan ƙwallon Borussia Dortmund kuma ɗan wasan gefe na matasa a Ingila, Jamie Gittens.(Jaridar Bild).
Ɗan ƙwallon Ingila Kobbie Mainoo mai shekaru 19, na ci gaba da tattaunawa da Manchester United domin sabunta kwangilarsa amma har yanzu ba a cimma matsaya ba. (Dan Jarida - Fabrizio Romano).
Ɗan wasan Porto da kuma Sifaniya Samu Omorodion mai shekaru 20, ya ce ƙaddara ce ta hana shi komawa Chelsea daga Atletico Madrid.(Jaridar Metro).
Bayern Munich ba ta sha'awar sayen golan Liverpool da Brazil Alisson Becker mai shekaru 32, duk da rashin tabbas a kan Manuel Neuer a kulob ɗin. (Talabijin ɗin ESPN).
Ɗan ƙwallon Chelsea da Ingila Reece James mai shekaru 24, na duba yiwuwar komawa Barcelona ko Benfica. (Jaridu da dama).










