Liverpool ta doke Chelsea 2-1 a Anfield

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta koma ta ɗaya kan teburin Premier bayan nasarar da ta samu kan Chelsea da ci 2-1 a Anfield.
Wannan ne wasa na 10 da kocin Arne Slot ya ci a duka gasanni tun farkon zuwansa ƙungiyar.
Liverpool ce ta fara cin kwallo a wasan bayan samun fenareti ta hannun Mohamed Salam a minti na 29 da fara wasan.
A minti na 48 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Chelsea ta farke wasan ya koma kunnan doki ta hannun Nicolas Jackson.
Curtis Jones ne ya ƙarawa Liverpool kwallo ta biyu da ta ba ta nasara a wasan kuma aka tashi 2-1.
Da kwallon da Mo Salah ya ci yanzu ya taimaka tare da cin kwallo 34 a duka wasanni, wanda rabon da a yi hakan tun lokacin Wayne Rooney da ya hada 36.
Yanzu maki ɗaya ne tsakanin Manchester City da ke ta biyu da kuma Liverpool da ke saman teburi. Maki hudu kuma tsakaninta da Aresnal da ke saman teburin a baya.
Yanzu Liverpool za ta buga wasanta na gaba ne da RB Leipzig ta Jamus a gasar Champions Lig a ranar Laraba.










