Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka za ta taƙaita yadda ƴanjarida ke samun bayanai a Pentagon
- Marubuci, Ben Hutton
- Aiko rahoto daga, Washington, DC
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta shaidawa ƴanjarida masu aiki a cikin ta cewa dole su amince da dokar haramta masu fitar da bayanan da hukumomi ba su bayar da izinin fitarwa ba ko kuma a hana su shiga ginin ma'aikatar.
Wannnan canji yana daga cikin sabbin dokokin ma'aikatar ta fitar da nufin taƙaita shige da ficen manema labarai a harabarta, inda ma'aikatar yaƙin Amurka da a baya aka fi sani da ma'aikatar tsaro ke da ofishi.
Ana alaƙanta wannan mataki da yadda ake samun fitar bayanan sirri daga ma'aikatar a watannin baya-bayan nan.
A saƙon da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Pete Hegseth, wanda kwanannan nan aka canza sunan muƙaminsa zuwa sakataren yaƙi ya ce ''ba manema labarai bane ke da ikon tafiyar da harkokin Pentagon-akwai waɗanda alhakin hakan ke kansu. Daga yanzu ba za a bari ƴanjarida na kai-kawo a cikin zauren ma'aikatar tsaro ba, ko dai su bi doka ko su tattara kayansu su koma gida.''
Sabuwar dokar tana ƙunshe ne a cikin wani saƙo da aka aikewa manema labarai da ke aiki a ma'aikatar, inda aka nemi su sanya hannu kan wata takarda ta nuna sun amince da dokar kafin ci gaba da gudanar da aikin su a ma'aikatar.
Ma'aikatar ta ce ''za ta ci gaba da aiki domin tabbatar da ƙa'ida da kiyaye amincin da jama'a suka ɗora mata''.
Ta ƙara da cewa ''Daga yanzu dole sai hukumomi sun amince da bayyana labari ko bayani ga jama'a sannan ƴanjarida za su iya fitar da shi.''
"Ƙa'idojin na nufin ƴanjarida da ke aiki a cikin Pentagon za su kiyaye dukkan dokoki da ƙa'idar aiki irin yadda ake yi a sauran cibiyoyin soji, ta yadda ba za su riƙa fitar da bayanan da hukumomi ke ganin cewa sun zamo bayanan sirri ba.
''Wannan ba wani abu bane illa sanya ƙa'idar aiki da za ta samar da yanayi mai kyau na tabbatar da tsaro ga dukkan jama'a da kuma ƙasa baki ɗaya.'' in ji kakakin Pentagon, Sean Parnell.
A baya dai Hegseth ya fuskanci suka a kan yadda ya yi sakaci da muhimman bayanan sirri da bai kamata su fita ga jama'a ba, inda ya yi kuskuren sakin bayanan yadda jami'an tsaro suka tsara kai hari a Yemen, cikin wani dandalin kafar Whatsapp a watan Maris.
Wata dambarwar ta sake tashi a watan Yuni, lokacin da aka fitar da wani bayanin sirri da ya ci karo da sanarwar gwamnati game da harin da Amurka ta kai a cibiyar nukiliyar Iran.