Wane ne Charlie Kirk wanda kisan shi ya janyo zargin juna a Amurka?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Shugaba Trump ya ce kisan daya daga cikin fitattun magoya bayansa - Charlie Kirk - mai rajin siyasa - wata bakar rana ce a tarihin Amurka.

An harbe shi ne a ranar Laraba yayin da yake jawabi wajen wata muhawara a jami'a a jihar Utah.

har yanzu ana can ana ta neman wanda ake zargi da harbin.

Kisan matashi Charlie Kirk wanda ya yi fice wajen iya kalamai da muhawara da ake gani tauraruwarsa na haskawa na ci gaba da janyo kalamai na alhini da suka ga kisan.

Mista Kirk mai shekara 31 wanda fitaccen mai rajin yada manufa da kare akidar masu ra'ayin rikau ne a siyasar Amurka da kuma Trump ke daukarsa a matsayin mai goyon bayansa na gani na fada.... ya gamu da ajalinsa ne a sanadiyyar harbin da aka yi masa a wuya a lokacin da yake jawabi a gangamin na jami'ar Utah Valley, taron da ya janyo takaddama a jami'ar.

A lokacin da aka harbe shi a wuya yana amsa tambayoyi ne a kan tashin hankali da ta'asa da ake yi da bindiga.

Harbin nasa ke da wuya sai wurin ya yamutse mahalatta taron suka rika ranta a na kare -ana in ba-ka-yi-ba-ni-wuri, yayin da jami'ai suka dauki Mista Kirk suka nufi asibiti da shi inda a can aka tabbatar da rai ya yi halinsa.

A wani sakon bidiyo Shugaba Trump ya bayyana cewa ya kadu tare da cika da alhini da bakin ciki na kisan gillar:

Ya bayyana shi a matsayin wanda aka kashe saboda fafutukar gaskiya da 'yanci tare da dora alhakin kisan nashi a kan tashin hankali na siyasa da abin da ya kira akidar tsattsauran ra'ayin sauyi ta haifar.

Gwamnan jihar ta Utah, Spencer Cox, ya ce Charlie Kirk ya gamu da kisan gilla ne na siyasa.

Mista Cox ya bayyana ranar a matsayin bakar rana ga jihar tasa, kuma ya nuna takaicin cewa kila wasu na murana da kisan mutumin da ya kira jigon siyasa.

Spencer Cox ya yi alkawarin gurfanar da duk wanda ke da hannu a lamarin.

Tsohon shugaban kasar na jam'iyyar Democrat, Barack Obama, ya yi tir da kisan da ya kira "abin kyama".

Ya ce kiyayya irin wannan ba ta gurbi a siyasar Amurka.

Sai dai gwamnan jihar Illinois, na jama'iyyar Democrat JB Prit-zker, ya ce kalaman shugaba Trump na taimakawa wajen rura wutar kiyayya a da'irar siyasar kasar.

Tun da farko jami'an tsaro sun tsare wasu mutane biyu na dan lokaci kan kisan inda bayan bincike suka sake su.

An rufe harabar jami'ar inda jami'an 'yansanda dauke da makamai ke ta kai-komo suna neman danbindigar a yankin.

Wane ne Charlie Kirk

Charlie Kirk ɗaya ne daga cikin manyan masu ra'ayin riƙau wanda ya yi suna a kafafen sadarwa a Amurka kuma na babban masoyin shugaba Donald Trump.

Kirk, mai shekara 31 da aka kashe a ranar Laraba a wani harbi da aka yi masa a jami'ar Utah ya yi fice wajen gabatar da muhawara da jawabi a makarantun Amurka.

A 2012, lokacin yana da shekara 18, yana cikin mutanen da suka kafa ƙungiyar Turning Point USA (TPUSA), wata ƙungiyar ɗalubai mai muradin yaɗa ra'ayin riƙau a makarantun Amurka.

Ya taso ne a cikin wadata Chicago inda ya fara karatu kafin ya shiga gwagwarmayar siyasa. Ya yi yunƙurin shiga aikin soji amma bai samu nasara ba.

Gudunmuwar sa ga ƙungiyar TPUSA ta fara bayyana ne bayan zaɓen shugaba Barack Obama karo na biyu a 2012.

Kafar CBS ta ruwaito cewa Kirk ya halarci taruka da dama na jam'iyar Republican kuma yana da miliyoyin mabiya a kafafen sada zumunta.

TPUSA ta taka gagarumar rawa wajen samun nasarar shugaba Trump da sauran ƴan jamiyyar Republican da suka yi nasara a zaɓen shekarar da ta gabata. Ana ganin Kirk ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen janyo hankalin dubban sabbin masu zaɓe domin su yi rijista, kuma ana ganin ya taimakawa shugaba Trump wajen lashe zaɓe a Arizona.

Ana kallon wasu daga cikin ra'ayoyinsa a matsayin masu tsauri. Ya riƙa kambama ɗabi'ar adawa da sauya jinsi da adawa da annobar Corona da kuma fitowa ƙarara yana iƙirarin cewa an sauya sakamakon zaɓen shugaban Amurka na 2020 domin kayar da shugaba Trump.

Ya kuma yi ƙaurin suna wajen bayyana ra'ayi mai cike da ruɗani game da yaƙin Gaza da kuma siyasar duniya.