Arsenal na kan bakarta game da Cunha, Barcelona ta tanadi kuɗin Rashford

Asalin hoton, Getty Images
Nottingham Forest ta mayar da hankali sosai kan neman ɗan wasan gaba na Wolves da Brazil, Matheus Cunha a wannan wata na Janairu a ƙoƙarinta na riƙe wuta domin ganin ta je gasar zakarun Turai ta Champions League. (Mail)
Arsenal ma ta nuna aniyarta ta sayo Cunha mai shekara 25 a wannan Janairu. (Fichajes)
Chelsea na shirin ci gaba da tattaunawa da Manchester United domin ɗaukar ɗan wasan Argentina, Alejandro Garnacho mai shekara 20, wanda aka yi wa kuɗi fam miliyan 50. (Telegraph)
Chelsea na son a zube mata tsabar kuɗi aƙalla Yuro miliyan 70 kafin ta bar ɗan wasanta na gaba ɗan asalin Fransa, Christopher Nkunku ya tafi Bayern Munich. (Sky Sports)
Ɗan wasan Manchester United da Brazil, Antony, mai shekara 24 na gab da kammala yarjejeniyar komawa Real Betis a matsayin aro. (Sky Sports)
Juventus da Borussia Dortmund na matsa ƙaimi domin ɗaukar ɗan wasan baya na Chelsea da Portugal, Renato Veiga, wanda a yanzu zai iya tafiya a matsayin aro ko kuma tafiyar dindindin. (Times)
Marseile ta zama ƙungiya ta baya-bayan nan da ta nuna sha'awar ɗaukar Marcus Rashford daga Manchester United. (L'Equipe)
Sai dai Rashford ya fi son tafiya Barcelona, ƙungiyar da a yanzu ta tanadi kuɗin da za ta iya ɗaukar matashin ɗan asalin Ingila. (Athletic)
Manchester City ta ta cimma yarjejeniyar baka da Real Valladolid mai buga gasar La Liga domin ɗaukar ɗan wasan tsakiya ɗan asalin Sierra Leone, Juma Bah, mai shekaru 18. (Fabrizio Romano)
Tsohon ɗan wasan Manchester United ɗan asalin Faransa, Paul Pogba ya ce ya ƙi amincewa da tayin wata ƙungiya da ta so ta ɗauke shi a Rasha. (Twitch)
Derby County ta shafa wa fuskarta toka ta yi fatali da tayin da Brighton ta yi mata na ɗaukar ɗan wasanta na tsakiya Eiran Cashin, mai shekara 23 a duniya. (Sky Sports)











