An yi ruwan ƙwallaye a wasan da Arsenal ta je ta doke West Ham

Bukayo Saka

Asalin hoton, Getty

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal ta koma ta biyu a teburin Premier League, bayan da ta je ta doke West Ham 5-2 a wasan mako na 13 a babbar gasar tamaula ta Ingila.

A minti na 10 da take leda Gunners ta zura ƙwallo da ka ta hannun Gabriel Magalhães, tun daga fara kakar bara Arsenal ta ci ƙwallo 20 daga ƙwana, kuma Gabriel ya ci na biyar daga ciki.

Daga nan sai Trossard ya kara na biyu, sannan Odegaard ya ci na uku, minti biyu tsakani Havert ya kara na huɗu, sannan Saka ya zura na biyar a raga.

Ita kuwa West Ham mai masaukin ɓaki ta ci biyu ne ta hannun Wan-Bissaka da wanda Emerson ya zura na biyu, tun kan hutu aka ci baƙwai a karawar.

Wannan shi ne karo na huɗu da aka zura ƙwallo baƙwai a wasa tun kan hutu, bayan na Blackburn da Leeds a Satumbar 1997 da na Bradford da Derby a Afirilun 2000 da na Reading da Manchester United a Disambar 2012.

Haka kuma karo na biyar da Arsenal ta ci ƙwallo biyar ko sama da haka a 2024, Sunderland ta taɓa yin irin wannan ƙwazon a 1892 da kuma Manchester City a 1937.

Arsenal, wadda ta ci wasa baƙwai da canjaras huɗu aka doke ta karawa biyu ta haɗa maki 25 tana ta biyun teburi.

West Ham kuwa tana ta 14, wadda ta ci karawa huɗu da canjaras uku aka doke ta karo na shida daga wasa 13 a Premier a kakar nan.