Real Madrid ta ƙi sakin Vinicius, Ajax na bibiyar Aaron Ramsdale

Vinicius Jr

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Brentford ta jajirce sai an biya ta aƙalla £60m a kan ɗan wasan gaban Ingila mai shekara 28, Ivan Toney, wanda Chelsea da Manchester United ke zawarci. (Independent)

Ajax na sha'awar ɗaukar mai tsaron gidan Arsenal da Ingila, Aaron Ramsdale, mai shekara 26. (Sky Sports)

Real Madrid ba za ta sakar wa gasar Saudi Pro League ɗan wasan gaban Brazil mai shekara 24, Vinicius Junior ba, ko da kuwa cinikin zai sa ya zama ɗan wasa mafi tsada a tarihi. (AS - in Spanish)

Al-Ittihad ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan tsakiyar Faransa, mai shekara 33, N'Golo Kante, duk kuwa da zawarcin sa da West Ham da Atlentico Madrid ke yi. (Fabrizio Romano)

Bournemouth na bibiyar ɗan wasan gaban Arsenal mai shekara 25, Eddie Nketiah domin cike giɓin da Dominic Solanke ya bari a ƙungiyar bayan sauya sheƙa zuwa Tottenham. (Mail)

Brighton ta gabatar da tayi kan ɗan wasan bayan Faransa mai shekara 26, Olivier Boscagli, amma PSV Eindhoven ta nemi ƙarin kudi kafin rabuwa da ɗan wasan nata. (Eindhovens Dagblad - in Dutch)

Leicester City ta gabatar da tayin £4m a kan ɗan wasan gaban Crystal Palace da kuma Ghana mai shekara 32, Jordan Ayew. (Mail)

Barcelona ta ƙi amincewa da tayin £23.9m da Everton ta gabatar mata a kan ɗan wasan gaban Brazil mai shekara 19, Vitor Roque. (Sky Germany)

Manchester United na shirin ɗaukar tsohon ɗan wasan bayan Chlesea da Sifaniya mai shekara 33, Marcos Alonso, wanda ya bar Barcelona tun bayan da kwangilar sa ta ƙare, kuma har yanzu bai samu wata ƙungiya ba. (Athletic - subscription required)

Napoli da RB Leipzig ne kan gaba a zawarcin ɗan wasan gaban Atletico Madrid mai shekara 20, Samu Omorodion bayan tattaunawar sauya sheƙarsa zuwa Chelsea ta rushe. (Football Insider)

Getafe ta fara harin ɗan wasan bayanTottenham da Ingila mai shekara 19, Ashley Phillips, wanda ta ke fatan ɗauka a matsayin aro. (Sky Sports)