Palmer ya tsawaita yarjejeniyarsa kaka biyu a Chelsea

Cole Palmer

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Cole Palmer ya saka hannu kan yarjejeniyar tsawaita zamansa a Chelsea zuwa kaka biyu, kenan zai ci gaba da taka leda a Stamford Bridge zuwa 2033.

Mai shekara 22 yana da ƙunshin yarjejeniya da Chelsea kaka tara kenan da cewar za a iya tsawaita masa, bayan rawar da ya taka a kakar da ta wuce.

Palmer ya ci ƙwallo 25 ya bayar da 15 aka zura a raga a wasa 45 a kakarsa ta farko a Chelsea, bayan da ya koma ƙungiyar kan £42.5m daga Manchester City.

Chelsea ta yaba da rawar da ɗan wasan tawagar Ingila ya taka a Euro 2024, wanda ya ci ƙwallo a wasan karshe da Sifaniya ta lashe kofin da cin 2-1 a Jamus.

Palmer yana cikin masu takarar ƙyautar gwarzon Premier League da kuma ta matashin gasar, inda ake sa ran bayyana zakara ranar Talata 20 ga watan Agusta.

Chelsea za ta fara wasan makon farko a Prremier League ta 2024/225 da karɓar bakuncin Manchester City a Stamford Bridge ranar Lahadi.

Chelsea za ta buga kakar bana da sabon koci, Enzo Maresca, wanda ya lashe Championship a bara, inda Leicester City ta samu gurbin shiga Premier ta bana.