Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙungiyoyin Saudiyya na farautar Vinicius Jr, Napoli ta taya Lukaku
Ƙungiyoyin Saudi Pro League na son ɗanwasan Real Madrid da Brazil mai shekara 24 Vinicius Jr. (ESPN)
Manchester United ta tattauna kan buƙatar ɗauko ƴanwasan gaba a bazara, da suka ƙunshi har da ɗanwasan Ingila da Everton Dominic Calvert-Lewin mai shekara 27. (Sky Sports)
Southampton ta amince ta sayar wa Hoffenheim ɗanwasan baya na Jamus mai shekara 22 Armel Bella-Kotchap kan fam miliyan 12.8, inda za diba lafiyarsa a ranar Talata. (Sky Sports)
Napoli ta taya ɗanwasan gaba na Chelsea da Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 31 kan fam miliyan 21.4 da ƙarin kuɗaden lada na fam miliyan 4.3m. (Gianluca di Marzio - in Italian)
Newcastle na diba zaɓin da ya rage mata kan ɗanwasan baya duk da sake taya ɗanwasan Crystal Palace da England Marc Guehi, mai shekara 24. (Athletic - subscription required)
Crystal Palace na sa ido kan ɗanwasan tsakiya na Chelsea Carney Chukwuemeka, mai shekara 20, kuma a shirye take ta taya idan an saka shi kasuwa. (South London Press)
Newcastle na farautar ɗanwasan Chelsea da Ingila mai shekara Noni Madueke idan har ƙungiyar ta Eddie Howe ta sayar da ɗanwasan tsakiya na Paraguay Miguel Almiron, mai shekara 30 ga Charlotte FC. (ipaper)
Red Bull Salzburg ta sake taya matashin ɗanwasan tsakiya na Liverpool Bobby Clark, mai shekara 19. (Times - subscription required)
Ana sa ran ɗanwasan baya na Wales Chris Mepham, mai shekara 26, zai bar Bournemouth a wannan bazara kuma Ipswich da Torino da Anderlecht duka sun nuna ɓukatar ɗanwasan. (Fabrizio Romano)
Leicester City ta cimma yarjejeniya da Bayer Leverkusen kan aron ɗanwasan gaba na Jamhuriyyar Czech Adam Hlozek. Amma sai ƙungiyar ta The Foxes ta amince da sauran sharuɗɗan yarjejeniyar. (Sky Germany)
Manchester United ta sake komawa tattaunawa da Everton kan ɗanwasan baya na Ingila mai shekara 22 Jarrad Branthwaite kan tayin kuɗi fam miliyan 60m. (Football Insider)
Manchester City a shirye take ta bayar da aron ɗanwasan Ingila mai shekara 28-Kalvin Phillips inda Ipswich da Everton da Fulham duka suka nuna suna so. (Manchester Evening News)
Aston Villa da Fulham da Crystal Palace na ribibin ɗanwasan Chelsea da Ingila Trevoh Chalobah, mai shekara 25. (Football Insider)