Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea za ta sake ɗaukar Felix na Atletico madadin Omorodion
Chelsea na auna yadda za ta sake ɗaunkar, Joao Felix daga Atletico Madrid, bayan da batun sayen Samu Omorodion ya ci karo da cikas.
An soke tattaunawa tsakanin Chelsea da Atletico kan cinikin Omodorion mai shekara 20, duk da cewar sun cimma yarjejeniyar £34.5m a tsakaninsu a makon jiya.
Tuni dai ƙungiyar ta Stamford Bridge ke ta ɗari-ɗarin sayen Omorodion, bayan da take fatan ɗaukar ɗan wasan Napoli Victor Osimhen, ta yi musaya da Romelu Lukaku.
Yanzu dai Chelsea na duba yadda za ta yi zawarcin Felix da sauran masu buga gurbin cin ƙwallaye, wadda ta tattauna da wakilin Felix.
Kawo yanzu Chelsea ta ɗauki ƴan wasa 10, wadda ta kashe £185m, wadda ke fatan karfafa ƙungiyar kan fara kakar bana.
Felix, mai shekara 24, na son komawa Stamford Bridge da taka leda, bayan wata shida da ya buga mata wasamnnin aro a 2022-23.
Atletico ta sayi Felix a mataki na biyar mafi tsada a tarihin ƙungiyar, wanda ta ɗauko daga Benfica £113m lokacin yana da shekara 19 a 2019.