Atletico ta kammala ɗaukar Alvarez daga Man City

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Atletico Madridta kammala ɗaukar ɗan wasan tawagar Argentina mai taka leda a Manchester City, Julian Alvarrez kan £81.5m kan yarjejeniyar kaka shida.

Ƙungiyar da Diego Simone ke jan ragama za ta biya £64.4m da karin tsarabe-tsaraben da zai kai £17.1m.

Mai shekara 24, shi ne mafi tsada da City ta sayar a tarihin ƙungiyar, bayan Raheem Sterling da Chelsea ta saya kan £50m a 2022.

City ta sayo Alvarez daga River Plate ta Argentina kan £14.1m a Janairun 2022.

Ya lashe kofi uku a kakarsa ta farko a Etihad da kofin duniya a Qatar a 2022 da Copa America a 2024.

Ɗan wasan tawagar Argentina zai koma Sifaniya da taka leda bayan cin ƙwallo 36 a wasa 106 da ya buga wa City.

City mai rike da Premier League na bara kuma hudu a jere, za ta fara da zuwa Chelsea a wasan makon farko a babbar gasar tamaula ta Ingila ta 2024/25.

Ita kuwa Atletico za ta je Villareal a karawar makon farko a La Liga ranar 19 ga watan Agusta.