Liverpool da Tottenham, Arsenal da Newcastle a gasar Carabao

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool da ke riƙe da kofin Carabao za ta fafata wasan kusa da na ƙarshe da Tottenham yayin da Arsenal za ta fuskanci Newcastle.
A wasan farko da za a yi, Liverpool da ke saman teburin Premier za ta je Spurs ne domin barje gumi kafin daga bisani a zo mata Anfield.
Ita kuwa Arsenal ita za ta fara karɓar baƙuncin Newcastle a filin wasa na Emirate a wasan farko, kafin daga bisani a je filin wasan St James' Park domin wasa na biyu.
Yadda aka raba jadawalin za a iya yin wasan hamayyar London a wasan ƙarshe wanda kuma zai iya ƙayatarwa.
Ba a taɓa buga wasan ƙarshe ba tsakanin Tottenham da Arsenal a wata babbar gasa ba, amma sun sha haɗuwa a League Cup a wasan kusa da na ƙarshe a shekarun 1968, 1987, 2007 and 2008.
Za a buga wasan farko ne ga gasar a ranar 6 ga watan Janairun 2025 sannan a buga na biyu a ranar 3 ga watan Fabirairun shekarar.
Wasan ƙarshe da za a buga a gasar za a yi sa ne ranar 16 ga watan Maris ɗin 2025 a filin wasa na Wembley.







