Chelsea da Arsenal na gogayya kan Sesko, Man United na zawarcin Ederson

Benjamin Sesko

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Chelsea na zawarcin ɗan wasan gaban RB Leipzig da Slovenia, Benjamin Sesko mai shekara 21. (Teamtalk)

A baya dai Arsenal ta tattauna kan yiwuwar ɗaukar Sesko kuma ta ci gaba da neman ɗan wasan bayan ƙulla kyakkyawar alaƙa da wakilansa. (Mail Plus)

Manchester United na nazari kan ɗan wasan tsakiyan Atalanta da Brazil, Ederson, mai shekara 25. (Florian Plettenberg)

West Ham da Leicester City da Southampton na fafatawa kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Brighton da Jamhuriyar Ireland, Evan Ferguson, mai shekara 20. (Givemesport)

Southampton za ta iya sayar da Tyler Dibling, mai shekara 18, idan ta rikito daga gasar Premier, inda Manchester United da Newcastle su ke zawarcin ɗan wasan tsakiyan na Ingila. (Football Insider)

An ƙaryata rade-radin cewa an ga tsohon ɗan wasan Manchester United da Juventus Paul Pogba mai shekaru 31 a filin atisayen Manchester City. (Fabrizio Romano)

West Ham da Fulham, da Crystal Palace duk suna nazari kan ɗan wasan Juventus Nicolo Fagioli, amma dan ƙasar Italiyan mai shekaru 23 ya ja hankalin Tottenham a baya kuma wataƙila zai gwammace ya koma ƙungiyar na arewacin Landan. (Tuttosport)

Kocin West Brom Carlos Corberan da tsohon kocin Denmark Kasper Hjulmand na daga cikin ƴan takarar da za su maye gurbin Russell Martin a Southampton, sai dai kocin rikon ƙwarya Simon Rusk ne zai ci gaba da jagorantar ƙungiyar a karawar za ta yi da Fulham ranar Lahadi. (Sky Sports)

Ɗan wasan Arsenal Reiss Nelson - wanda a halin yanzu yake zaman aro a Fulham - za iya barin Gunners a bazara mai zuwa bayan an tabbatar da cewa ɗan wasan mai shekara 25 ba ya cikin tsarin Mikel Arteta. (Mail Plus)

Tsohon kociyan Coventry Mark Robins ya ƙi amincewa da damar tattaunawa da Millwall game da gurbin kocin da ke akwai kulob ɗin. (South London Press)

Valencia da Real Betis da Villarreal duk suna nazarin ɗaukar ɗan wasan tsakiyan Brazil Arthur Melo, mai shekara 28, daga Juventus. (Gianluca di Marzio)

Ɗan wasan Monaco da Faransa Magnes Akliouche, mai shekara 22, ya ce zai so ya taka leda a Barcelona. (Sport)