''Man City na bukatar kara kwazo domin sake lashe Premier League''

An wallafa

John Stone ya amince cewar lallai sai sun kara kwazo a wasanninsu, idan suna son sake lashe kofin Premier League a kakar nan.

Arsenal, wadda ta ci Manchester United 3-2 a ranar Lahadi a babbar gasar tamaula ta Ingila tana da maki 50 da tazarar biyar tsakaninta da Manchester City ta biyu.

Ranar Lahadi City ta doke Wolverhampton da ci 3-0 a Etihad, kuma Erling Haaland ne ya ci kwallaye uku rigis, karo na hudu a Premier League a Etihad.

Haaland ya fara cin Crystal Palace kwallo uku da Nottigham Forest da kuma Manchester United a kakar nan.

Cikin fushi a cikin mutane Pep Guardiola ya ce 'yan wasansa na bukatar zage damtse, bayan da Tottenham ta ci su 2-0 daga baya suka farke suka lashe karawar ranar Alhamis.

Guardiola ya bayyana fushinsa karara ga 'yan wasan, bayan rashin nasara a hannun Manchester United a wasan hamayya a Premier, sannan Southampto ta fitar da su daga Carabao a kakar nan.

Har yanzu City ba ta fuskanci Arsenal ba a Premier League, amma za su fafata a FA Cup ranar Juma'a 27 ga watan Janairu.