Bukukuwan Babbar Sallah a cikin hotunan Afirka na mako

.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ƙwararren ɗan wasan gargajiya daga Moallem Houssem Ghina ya daka tsalle don nishaɗantar da jama`a gurin gasar waƙoƙi ta duniya a Moroko.
An wallafa
,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mai sana`ar kamun kifi ya na gyaran kifi a tsibirin Zanzibar domin kaiwa kasuwar kifi ta garin Stone wadda take ci a ranakun Juma`a.
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An fara shagulgulan bikin Sallah a yankunan Adjame dake Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast tun ranar Talata, jajiberen Babbar Sallah.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Iyalai a Masar sun dauki hoto da gwaggon biri a harabar masallacin babban birnin kasar.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mutum yana fiɗar ragon Sallah a Wad Hamid dake Arewacin Khartoum babban birnin kasar Sudan, al`umma sun gudanar da bukukuwan Sallah duk da rikici a kasar.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mai Ibada a masallacin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu ranar Alhamis, bayan an kammala shagalin bikin Sallah.
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ana shafawa ɗan kasar Saliyo tawada bayan ya kaɗa kuri`a a zaben kasar da ya gudana a ranar Asabar.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan Shugaba Julius Maada Bio a birnin freetown na farin cikin nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar, sakamakon zaben da ƴan adawa su ka ce ba su amince da shi ba.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin Madagasca sun yi fareti a birnin Antananarivo ranar litinin, lokacin bikin cikar kasar shekaru 63 da samun ƴancin kai.
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Jagoran Adawa a kasar Kenya Raila Odinga ya gwada farin jininsa a ranar Talata, ta hanyar kiran al`umma su bijire wa dokar karin kuɗaɗen haraji.