Babban fasto ɗan Najeriya da ke sa jama'a su ƙyamaci rigakafin malaria

Asalin hoton, Pastor Chris Online
- Marubuci, By Chiagozie Nwonwu, Fauziyya Tukur, and Olaronke Alo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Global Disinformation Team
- An wallafa
Sanye da kayan da ya fi shahara da su na kwat mai zagayayyen wuya, Fasto Chris Oyakhilome, na kallon kyamara kai-tsaye lokacin da ya yi iƙirarin cewa "babu wata hujjar da ke tabbatar da sahihancin alluran rigakafi".
Ana yi wa mutane "ƙarya ne kawai" game da rigakafi, in ji shi yayin wata huɗuba da aka yaɗa a tasharsa ta dandalin YouTube a watan Fabrairu.
Mista Oyakhilome mai shekara 60 wanda kuma aka fi sani da Fasto Chris, ɗaya daga cikin mafiya shahara a masu wa'azin Kiristanci a nahiyar Afirka. BBC ta bi diddigin huɗubobinsa a 2023 da 2024 kuma ta gan yadda ya dinga yaɗa adawa da rigakafi ga mabiyansa, musamman kan sabuwar rigakafin zazzaɓin maleriya da aka fara yi a Afirka.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), an samu kashi 95 cikin 100 na mutanen da suka mutu saboda maleriya a Afirka a 2022 - inda yara ne kashi 80 cikin 100 na mamatan.
Cikin wata shida da suka wuce, kamfanin Mista Oyakhilome ya kuma shirya finafinan adawa da rigakafi aƙalla biyar masu tsawon minti 20 da aka yaɗa a wa'azin coci ko kuma aka wallafa a shafinsa na intanet, wanda hakan ya saɓa wa ƙa'idojin amfani da shafukan sada zumuntar.
Zargin rage yawan al'umma
Sanarwar da aka bayar ta fara amfani da rigakafin maleriya - bayan shafe shekaru ana yunƙuri - ta samu yabo a matsayin babban cigaba da zai iya ceto rayukan dubban mutane.
A cewar asusun yara na Majalaisar Ɗinkin Duniya (Unicef), matakin ya taimaka wajen raguwar kashi 13 cikin 100 na mutuwar yara daga maleriya bayan ƙaddamar da rigakafin a 2019 a ƙasashen Kenya, da Ghana, Malawi.
Sai dai ƙwararru a harkokin lafiya na fargabar tasirin huɗubobin Fasto Chris zai iya shafar karɓar rigakafin a Afirka.
A watan Agustan da ya gabata, faston ya yi gargaɗi a wata huɗubarsa kan "wani mugun shiri da aka daɗe ana yi". Sai kuma ya yi wani shaci-faɗi da aka saba yi: cewa ana amfani da rigakafi ne don "rage yawan al'ummar duniya".
Haka nan, ya kuma yi iƙirari maras tushe cewa "maleriya ba ta taɓa zama matsala ga 'yan Afirka".

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Yaɗa labaran ƙarya game da rigakafi, musamman shugabannin addini, zai iya taimakawa wajen cigaban ƙarairayi da rashin fahimta, da kuma ta'azzara ƙiyayyar rigakafi. Hakan zai iya yin mummunan tasiri kan harkokin lafiyar al'umma, musamman a WHO ta Afirka inda ake yawan samun cutukan da ake iya samun kariya," in ji mai magana da yauwn WHO.
An saka maganganun Fasto Chris cikin abubuwan da suka kamata a saka wa ido kafin fito da rigakafin a watan rahoton watan Maris da cibiyar The Africa Infodemic Response Alliance ta fitar, wadda WHO ta kafa.
Mun tambayi Fasto Chris game da maganganunsa kan rigakafi ta adireshin imel na kamfani da kuma cocinsa, amma ba mu samu amsa ba.
Faston ya kafa cocin Christ Embassy a Legas a shekarun 1990 kuma tun daga nan ya dinga samun dubundubatar mabiya a faɗin duniya.
A 2011, mujallar Forbes ta saka shi cikin fasto-fasto mafiya arziki a Najeriya, inda darajar arzikinsa ta kai dala miliyan 30 zuwa 50.
A cewar mujallar, harkokin faston sun ƙunshi jaridu, da mujalloli, da tashar talabijin, da kamfanin ɗab'i, da tashar tauraron ɗan'adam, da otel-otel, da kuma kamfanin gine-gine.
Kamfaninsa mai suna LoveWorld Inc ya haɓaka sosai. Yanzu ya ƙunshi dandalin yaɗa labarai nasa intanet, da manhajar aika saƙonnin da mutane sama da miliyan ɗaya ke amfani da ita, da kuma bankin ba da rance.
'Buƙatar a jawo hankali'
A cewar shafin intanet na cocinsa, mutum kusan biliyan bakwai ne ke sauraron wa'azinsa a faɗin duniya - sai dai wannan abu ne mai wuya saboda ita kanta al'ummar duniyar an yi ƙiyasin ba ta wuce biliyan takwas ba.
Winnifred Ikhianosin mai shekara 25 na yawan halartar cocin. Ta faɗa wa BBC cewa ta ƙi yarda a yi mata rigakafi. "Malamin ne ya faɗa mana," in ji ta. "Kuma ni ma na yi nawa binciken."
Ada Umenwalir, wata jagora a cibiyar nazarin Afirka da ke Jami'ar North Carolina a Chapel Hill, ta ce Fasto Chris "na da babban tasiri kan mabiyansa da ke koyi da shi".
"Fasto-fasto da malaman addini za su ci gaba da taka rawa mai girma game da ra'ayoyin mabiyansu," in ji ta. Amma talauci da ƙarancin kyawawan cibiyoyin lafiya a Afirka, a cewarta, za su iya taimakawa wajen cimma muradan cocin a kan al'umma.
"Akwai buƙatar mu yi gargaɗi yanzu. Aƙidar da Fasto Chris ke yaɗawa na da haɗari kuma ba ta da alaƙa da addinin Kirista," a cewar marubuci Julius Ogunro, wanda ya saba halartar wa'azin Chris tsawon shekara 10.
Akwai sunan mutum ɗaya da faston ke yawan fada: Bill Gates. Hamshaƙin mai arzikin na cikin mutanen da ke ɗaukar nauyin samar da rigakafin maleriyar, amma kuma an sha alaƙanta shi da ƙairayi game da rigakafin tsawon shekaru.

Asalin hoton, AFP
Yayin wani wa'azi a Agustan 2023, Chris ya nuna wani bidiyo na Bill Gates yana magana ta cikin shirin TED talk a 2010 a matsayin "waɗanda ke da shirin rage yawan al'ummar duniya".
Da yake magana kan rage yawan iskar gas mai gurɓata muhalli, Mista Gates ya ce: "Da farko, muna da yawan al'umma. Duniya na da al'umma biliyan 6.8 yanzu. Da alama sun kama hanyar zama biliyan tara. Idan muka yi ƙoƙari sosai kan rigakafi, da kiwon lafiya, da haihuwa, za mu iya rage yawan da kamar kashi 10 ko 15 cikin 100."
Faston ya sauya wa maganarsa ma'ana. Mista Gates bai nemi a rage yawan al'umma ba. Ya jaddada a baya cewa yana ganin ƙaruwar al'umma da kuma kyautata kiwon lafiya abu ɗaya ne: "Idan kiwon lafiya ya kyautata, iyalai za su so su rage haihuwa."
Fasto Chris ya ce ginin cibiyar World Mosquito Program da ke Colombia na Gidauniyar Gates ne, yana zargin ta da ƙirƙirar sauron da aka sauya wa ƙwayoyin halitta don rage wa al'ummar duniya yawa.
Ma'aikatar da aka ƙirƙira don rage wa sauro ƙarfin yaɗa cutuka, ta wata ƙungiya ce mallakin Jami'ar Monash da ke Australiya, kuma ta bayyana ƙarara cewa babu maganar sauya wa sauro ƙwayoyin halitta a ayyukanta.
Da ma faston ya saba yaɗa adawa da rigakafi da labaran ƙarya. A kwanan nan ya kai wa rigakafin cutar kansar mahaifa (HPV), wadda ke kare mata daga kansar bakin mahaifa.
"Suna da wata manufa ne, ba maganar kansa ba ce," in ji Fasto Chris yayin wani wa'azinsa da aka yaɗa ranar 2 ga watan Satumban 2023.
A watan Oktoban 2023 ne Najeriya ta fara yi wa 'yan mata rigakafin don kare su daga kansar bakin mahaifa. Cutar na kashe mata sama da 8,000 a Najeriya duk shekara. A 2021, binciken da cibiyar Cancer Research UK ta ɗauki nauyi ya nuna cewa rigakafin na rage kamuwa da cutar da kusan kashi 90 cikin 100 a Najeriya.
A baya dai, faston ya sha yin iƙirari marasa tushe kan alluran cutar tetanus, da polio, da sauran rigakafin yara.
Haka nan, ya yi ƙaryar cewa rigakafin da aka haɗa da fasahar RNA na sauya ƙwayoyin halittar mutum.
Amma rigakafin ba ta sauya wa mutum ƙwayar halitta. Tana ɗaukar wani ɓangare ne na ƙwayoyin halittar cutar don koya wa garkuwar jikin ɗan'adam dabarun yadda za ta gane cutar kuma ta murƙushe ta.
A lokacin annobar korona, hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta Birtaniya, Ofcom, ta ci tarar cocin faston fan 125,000 - kwatankwacin dala 155,000. Ta ce tasharsa ta Loveworld da ke yaɗa shiri a Birtaniya ta yaɗa "bayanan boge ko kuma cutarwa game da annobar korona da kuma rigakafinta".
Mista Ogunro, marubucin da ya daina zuwa cocin, ya ce akwai damuwa.
"Iƙirarinsa kan rigakafi na tsorata ni. Akwai buƙatar mu saka dokoki kan masu wa'azi kamarsa."











