Kamaru ta samu gurbin zuwa buga kofin Afirka a 2024

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Kamaru ta samu gurbin shiga gasar kofin nahiyar Afirka da za a buga a 2024, bayan da ta ci Burundi 3-0 ranar Talata.
Tawagogin sun kammala minti 45 din farko ba ci, kuma baki, Burundi sun sa matsi sai sun doke Kamaru har gida, amma Andre Onana ya hana.
Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Kamaru ta fara cin kwallo ta hannu Bryan Mbeumo, sannan Christopher Wooh ya kara na biyu.
Daf da za a tashi daga wasan ne, Vincent Aboubakar ya kara kwallo na uku.
Ranar 9 ga watan Yuni, Kamaru ta je ta ci Burundi 1-0 a wasan cikin rukuni a wasan na neman shiga gasar nahiyar Afirka.
Da wannan sakamakon Kamaru ta zama ta daya a kan teburin rukuni na uku da maki bakwai, sai Namibia ta biyu mai maki biyar.
Burundi ta karkare a mataki na uku da maki hudu, bayan da aka kori Kenya, wadda Fifa ta dakatar da ita, bayan da gwamnati ta saka baki a harkokin tamaula.
Karo na 21 da Indomitable Lions za ta je ta buga babbar gasar tamaula ta Afirka, wadda ta karbi bakuncin wasannin da aka yi a 2021.
Kamaru mai rike da kofin nahiyar Afirka karo biyar, ta dauka a 1984, da 1988 da 2000 da 2002 da kuma 2017, ita ce ta biyu a yawan daukar kofin, bayan Masar mai bakwai jimilla.
Senegal ce mai rike da kofin da ta lashe a Kamaru a karon farko a tarihi da ta samu daukar kofin, bayan da ta ci Masar 4-2 a bugun fenariti.
Kawo yanzu an samu tawaga 24 da za su kece raini a Ivory Coast da za a fara cikin Janairun 2024.
Tawagogin sun hada da Najeriya, Guinea-Bissauda, Burkina Faso, Cape Verde, Masar, Guinea, Ghana, Angola, Algeria, Tanzania, Mali, Gambia da kuma Zambia.
Sauran sun hada da Jamhuriyar Dumukradiyyar Congo, Mauritaniya, Tunisia, Equatorial Guinea, Afirka ta Kudu, Morocco, Mozambique, Namibia da Kamaru da mai rike da kofin Senegal.
Ivory Coast, wadda za ta karbi bakuncin tana da gurbi kai tsaye.
Cikin Janairun 2024 za a fara tata burza a babbar gasar tamaula ta Africa.

Asalin hoton, Getty Images











