Frank Ribery ya yi ritaya daga sana'ar kwallon kafa

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon dan kwallon, Bayern Munich ta tawagar Faransa, Franck Ribery ya sanar da yin ritaya daga sana'ar tamaula.
Mai shekara 39, ya soke sauran kunshin kwantiraginsa da kungiyar da ke buga Serie A, Salernitana, bayan da yake fama da jinyar raunin gwiwar kafa.
Ya ci kwallo 124 ya kuma bayar da 182 aka zura a raga a wasa 425 da ya yi wa Bayern Munich tsakanin 2007 zuwa 2019.
Dan kasar Faransa ya lashe Bundesliga tara da Champions League a 2013.
Ribery ya fara zuwa Fiorentina daga nan ya koma Salernitana a bara, wanda ya taimaka kungiyar ba ta fadi daga Serie A da maki daya tal tsakani ba.
Sai dai bai sake buga wasa ba tun bayan wanda kungiyar ta fara da Roma ta kuma sha kashi a wasan farko a Serie A.
An dade ana ta rade-radin zai yi ritaya, yanzu ya sanar da kansa cewar ya rataye takalmansa na taka leda.
Dan kasar Faransa ya koma Bayern Munich kan £17m daga Marseille a cikin watan Yunin 2007, kaka daya tsakani da ya kasance cikin 'yan kwallon tawagar Faransa da suka yi na biyu a gasar kofin duniya da Italiya ta dauka a 2014.
Wanda ya lashe kyautar gwarzon dan Faransa karo uku ya ci mata kwallo 16 a wasa 25 da ya yi mata, wanda ya yi ritaya daga buga mata wasanni a 2014.
Bayan kaka 12 da ya yi a Bayern Munich ya bar kungiyar tare da Arjen Robben bayan da Bayern da lashe Bundesliga na bakwai a jere a lokacin.









