Messi da Neymar da Mbappe sun ci kwallo 43 a tsakaninsu a bana

An wallafa

Ranar Asabar Paris St Germain ta doke Troyes da ci 4-3 a wasan mako na 13 a gasar Ligue 1, inda Lionel Messi da Neymar da Kylian Mbappe sun ci kwallaye.

Messi da Neymar kowanne ya ci ya kuma bayar aka zura a raga, bayan da Carlos Soler ya fara ci wa PSG, sannan Mbappe ya zura na hudu a bugun fenariti.

Ita kuwa Troyes ta ci kwallaye ta hannun Ante Palaversa daf a tashi da kuma Tanguy Zoukrou da ya fara cin biyu tun farko.

Kawo yanzu yan wasan uku sun zura kwallo 43 a tsakaninsu a kakar nan, har da 11 ta Mbappe da 10 ta Neymar da bakwai da Messi suka ci a Ligue 1 kawo yanzu.

Dukkan 'yan wasan hudu sun ci kwallo a wasan da PSG ta doke Maccabi Haifa 7-2 a Champions League da tuni ta kai zagayen gaba.

PSG mai rike da kofin Ligue 1 guda 10, wadda ba ta yi rashin nasara a bana a dukkan fafatawa ba, za ta fuskanci Juventus a wasan karshe a rukuni na takwas ranar Laraba.

Idan PSG ta yi nasara a wasan zai ba ta damar jan ragamar rukunin zuwa wasannin kungiyoyi 16 da za su ci gaba da kece raini a gasar Zakarun Turai ta bana.