Real za ta buga La Liga da Champions League da Copa a Maris

Asalin hoton, Real Madrid FC
Real Madrid na shirin buga wasa a La Liga da Champions League da kuma Copa del Rey a cikin watan Maris.
Za ta fara karbar bakuncin Barcelona a wasan farko a daf da karshe a Copa del Rey ranar Alhamis a Santiago Bernabeu.
Ranar Lahadi kuwa Real za ta ziyarci Real Betis, domin fafatawa a wasan mako na 24 a La Liga ranar Lahadi.
Ranar 3 ga watan Satumba Real ta ci Betis 2-1 a Santiago Bernabeu a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Daga nan Real za ta karbi bakuncin Espanyol a fafatawar mako na 25 a La Liga, Real ce ta je Espanyol ta ci 3-1 cikin watan Agusta a wasan farko a kakar nan.
Bayan nan Real za ta karbi bakuncin Liverpool a wasa na biyu a Champions League a Santiago Bernabeu.
Liverpool ta yi rashin nasara da ci 5-2 a hannun Real ranar 21 ga watan Fabrairu a Anfiled a wasan farko zango 'yan 16 a Champions League.
Daga nan Barcelona za ta karbi bakuncin Real a wasan mako na 26 a La Liga, an ci Barca 3-1 ranar 16 ga watan Oktoba a wasan farko.
Ko da yake Barcelona ta doke Real Madrid 3-1 a cikin watan Janairu ta lashe Sifanish Super Cup a Saudi Arabia.
Jerin wasannin da Real Madrid za ta buga a cikin watan Maris:
Ranar Alhamis 2 ga watan Maris
- Real Madrid da Barcelona Copa del Rey daf da karshe wasan farko
Ranar Lahadi 5 ga watan maris
- Betis da Real Madrid LaLiga wasan mako na 24
Ranar Asabar 11 ga watan Maris
- Real Madrid da Espanyol LaLiga wasan mako na 25
Ranar Laraba 15 ga watan Maris
- Real Madrid da Liverpool Champions League karo na biyu
Ranar Lahadi 19 ga watan Maris
- Barcelona da Real Madrid LaLiga wasan mako na 26









