Real za ta buga La Liga da Champions League da Copa a Maris

An wallafa

Real Madrid na shirin buga wasa a La Liga da Champions League da kuma Copa del Rey a cikin watan Maris.

Za ta fara karbar bakuncin Barcelona a wasan farko a daf da karshe a Copa del Rey ranar Alhamis a Santiago Bernabeu.

Ranar Lahadi kuwa Real za ta ziyarci Real Betis, domin fafatawa a wasan mako na 24 a La Liga ranar Lahadi.

Ranar 3 ga watan Satumba Real ta ci Betis 2-1 a Santiago Bernabeu a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Daga nan Real za ta karbi bakuncin Espanyol a fafatawar mako na 25 a La Liga, Real ce ta je Espanyol ta ci 3-1 cikin watan Agusta a wasan farko a kakar nan.

Bayan nan Real za ta karbi bakuncin Liverpool a wasa na biyu a Champions League a Santiago Bernabeu.

Liverpool ta yi rashin nasara da ci 5-2 a hannun Real ranar 21 ga watan Fabrairu a Anfiled a wasan farko zango 'yan 16 a Champions League.

Daga nan Barcelona za ta karbi bakuncin Real a wasan mako na 26 a La Liga, an ci Barca 3-1 ranar 16 ga watan Oktoba a wasan farko.

Ko da yake Barcelona ta doke Real Madrid 3-1 a cikin watan Janairu ta lashe Sifanish Super Cup a Saudi Arabia.

Jerin wasannin da Real Madrid za ta buga a cikin watan Maris:

Ranar Alhamis 2 ga watan Maris

  • Real Madrid da Barcelona Copa del Rey daf da karshe wasan farko

Ranar Lahadi 5 ga watan maris

  • Betis da Real Madrid LaLiga wasan mako na 24

Ranar Asabar 11 ga watan Maris

  • Real Madrid da Espanyol LaLiga wasan mako na 25

Ranar Laraba 15 ga watan Maris

  • Real Madrid da Liverpool Champions League karo na biyu

Ranar Lahadi 19 ga watan Maris

  • Barcelona da Real Madrid LaLiga wasan mako na 26