Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a yi karon-batta tsakanin Liverpool da Chelsea ranar Laraba
Liverpool za ta karbi bakuncin Chelsea a wasan mako na 22 a gasar Premier League ranar Laraba a Anfield.
Ranar 13 ga watan Agustan bara kungiyoyin sun tashi 1-1 a Stamford Bridge, inda Luis Diaz ya fara ci wa Liverpool kwallo daga baya Chelsea ta farke ta hannun Axel Disasi.
Liverpool tana matakin farko a kan teburin Premier da maki 48, bayan karawa 21.
Chelsea ma wasa 21 ta buga, tana mataki na tara da maki 31 a babbar gasar tamaula ta Ingila.
A daren Talata Arsenal za ta je gidan Nottingham Forest, bayan da Gunners mai maki 43 take ta ukun teburi.
Manchester City mai maki 43 iri daya da na Arsenal za ta karbi bakuncin Burnley a ranar Laraba a Etihad.
A makon jiya ne kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya sanar cewar zai ajiye aikin horar da kungiyar a karshen kakar nan.
Hakan ne ya sa kyaftin ɗin kungiyar Virgil van Dijk ya ce bai san makomarsa ba a Anfield da zarar ɗan kasar Jamus din ya yi murabus.
Sai dai ɗan tawagar ta Netherlands ya ce ya kamata kungiyar ta fuskanci kalubalen da ke gabanta da lashe kofunan kakar nan, domin taya Klopp murnar kammala aiki.
Liverpool, wadda take ta daya a kan teburin Premier League ta kai wasan karshe a Carabao Cup da samaun gurbin mataki na biyar a FA Cup.
Haka kuma kungiyar ta Merseyside ta kai zagaye na biyu a gasar zakarun Turai ta Europa League.
Wasannin mako na 22 da za a buga a Premier League ranar Laraba:
- Manchester City da Burnley
- Tottenham da Brentford
- Liverpool da Chelsea