Tsugunne ba ta ƙarewa Manchester United ba

Asalin hoton, Getty Images
Masana na ci gaba da tsokaci a kan yadda makomar Manchester United da aka kora daga Gasar Zakarun Turai, za ta kasance.
Wasu na ganin wahalar ƙungiyar ta ƙare domin babu wani kofin Turai da take bugawa, za ta mayar da hankalinta ne kawai kan gasar Premier ta cikin gida.
Sai dai cikin wasa takwas da za ta buga na gasar, biyar a cikinsu na da matuƙar hatsari domin kuwa za ta fafata da Liverpool, akwai Aston Villa wadda za ta gamu da ita sau biyu, akwai Tottenham da kuma West Ham.
Baya ga ƙarfin da waɗannan ƙungiyoyi ke da shi, akwai wata matsala ta jinya da ƙungiyar ke ɗawainiya da ita.
Akwai 'yan wasa kusan 11 da duka ba sa cikin waɗanda suke mata wasa, cikinsu har da Tyrell Malacia da Lisandro Martínez da Christian Eriksen da kuma Anthony Martial.
Sauran sun haɗa da Mason Mount da Casemiro da Jadon Sancho da Marcus Rashford da dai sauransu.
Babu shakka rabin waɗannan 'yan wasa suna cikin goma sha ɗayan farko da Man United ta dogara da su.
Baya ga wannan matsala, sai wadda ke neman kassara kulob ɗin gaba ɗaya kamar yadda masu bibiyar ƙwallon ƙafa ke bayyanawa.
Wato, rashin jituwar da ake samu tsakanin mai horas da ƙungiyar Erik Ten Hag da 'yan wasansa.
An ta samun labarai masu cin karo da juna kamar su: Man United ta hana ƴan jarida zuwa hira da Erik ten Hag.
Akwai wani labari da shi da kansa kocin ya bayyana cewa: Ba mu da rarrabuwar kai a United - Ten Hag.
Sai ɗaya daga cikin 'yan wasan ƙungiyar da ya fito ya ce : 'Yan wasan Man United na goyon bayan Ten Hag - McTominay.
Bahaushe na cewa babu rami mai ya kawo maganar rami? ma su nazari na ganin matuƙar ana so Manchester United ta dawo kan ƙadaminta sai an kawo ƙarshen wannan matsala.
Babu wata ƙungiya da take samun nasara da rabuwar kai tsakaninta.











