Man United ta hana ƴan jarida zuwa hira da Erik ten Hag

Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United ta hana ƴan jarida zuwa taro hudu na ganawa da Erik ten Hag tun daga ranar Talata.

United ta yi korafin ba a ba ta damar mayar da martani da ya shafi kungiyar a labaran da zai zubar mata da kima.

Sai dai hukuncin bai shafi ƴan jarida daga Sky da ESPN da Manchester Evening News da kuma Mirror ba, wadanda suka bayar da rahoton cewa ƴan wasa ba sa jin dadin taka leda karkashin Ten Hag.

''Muna daukar matakan da suka da ce a kan kafafen yada labarai,'' kamar yadda kungiyar ta sanar.

''Ba wai ba ma son a wallafa labarin mu ba ne, amma wasu na yi ba tare da tuntubar mu don jin bangaren mu ko ba mu damar kalubalantar wasu labaran.

''Muna jin wannan mataki ne mai mahimmaci don kare kanmu da fatan zai samar da martabar da muke yi wa juna a bana, kamar yadda muke aiki.''

United, wadda take mataki na bakwai a teburin Premier League za ta karbi bakuncin Chelsea a Old Trafford a wasan mako na 15 ranar Laraba.