Barcelona na zawarcin Haaland, Arsenel na son Ousmane

An wallafa

Ɗan wasan gaba da ke kai hari a Manchester City Erling Haaland ya kasance wanda Barcelona ke hari a kakar wasan 2025. Wakilin matashin mai shekara 23, Rafaela Pimenta, ya gana da babban jami'i ƙungiyar ta La liga da ke kula da harkokin wasanni, Deco, a watan da ya gabata. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Mai bugawa Brentford da Ingila gaba, Ivan Toney ɗan shekara 28, na iya kasancewa zaɓin Manchester United a wannan kakar. (Fabrizio Romano via Caught Offside)

United na son saye ɗan wasan Wolves' da Brazil mai shekara 23 Joao Gomes domin maye gurbin fitaccen ɗan wasanta Casemiro, mai shekara 32. (Sport - in Spanish)

Arsenal ta samu kwarin gwiwa kan yiwuwar saye ɗan wasan Newcastle da Sweden, Alexander Isak bayan ɗan wasan mai shekara 24 ya amincewa cewa komai na iya faruwa a kasuwar cinikin 'yan wasa. (Mail)

Kungiyar da ake yi wa lakabi da 'The Gunners' na duba yiwuwar saye ɗan wasa daga Sporting Lisbon da Ivory Coast, Ousmane Diomande, mai shekara 20, da ke buga tsakiya bayan bajintar da ya nuna a lokacin da suka je farautar ɗan wasan gaban Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 25. (Sun)

Gyokeres yanzu ya sha gaban ɗan wasan Ingila da Brentford Ivan Toney a zabin Arsenal, yayin da ita ma West Ham ta nuna zawarcinta. (TalkSport)

Manchester United za ta kasance cikin cikakken tawagar jami'an horarwa, idan suka dau Gareth Southgate a matsayin koci a sabuwar kaka. (Sun)

Amma United na son ganawa da kocin Wolves Gary O'Neil kan ba shi aiki a Old Trafford. (ESPN)

Tsohon kocin Chelsea da Manchester United da Tottenham, Jose Mourinho ya ce a shirye yake ya dawo aikinsa bayan bankwana da Roma. (Fabrizio Romano)

Duk da son da suke yiwa kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso, Liverpool da Bayern Munich sun kuma kwaɗaitu da kocin Brighton, Roberto de Zerbi. (Bild - in German)

Mahaifin Luis Diaz ya ce, ba su fid da rai ba kan burin ɗan wasan na Liverpool da Colombia, mai shekara 27 na taka leda a Sifaniya. (Cadena SER - in Spanish)

Wolves na kan gaba a fafatawar saye ɗan wasan Southampton da Scotland, Che Adams, mai shekara 27, idan kwantiragin da yake kai ya kare. (Telegraph - subscription required)

Ajax na duba yiwuwar cimma yarjejeniya kan ɗan wasan Aston Villa, mai shekara 20, Tim Iroegbunam. (Football Insider)

Sturm Graz na son dauko ɗan wasan Arsenal da Denmark, Mika Biereth, mai shekara 21, a yarjejeniyar dindindin. (Evening Standard)

Gunners a shirye suke su sayar da ɗan wasansu na baya asalin kasar Portugal, Nuno Tavares, mai shekara 24, a wannan kaka. (Football London)

Chelsea za ta saurari tayi kan ɗan wasan Ingila mai shekara 24, Conor Gallagher da ɗan wasan baya Trevor Chalobah, mai shekara 24 da kuma ɗan wasanta na Albania mai shekara 22, Armando Broja a wannan kaka yayinda suke kokarin kaucewa saba dokokin Firimiya. (Football Insider)

Brighton na farautar ɗa wasan Najeriya mai shekara 24, Philip Otele, da ke taka leda a kungirae Cluj ta Romania. (Evening Standard)

Real Madrid ta shiga farautar ɗan wasan Argentina mai shekara 16, Franco Mastantuono. (90min)