Man Utd na son Kubo, Chelsea ba ta sha'awar Ramsdale

An wallafa

Manchester United na son sayen dan wasan gaba na gefe na Real Sociedad Takefusa Kubo, dan Japan mai shekara 22, domin maye gurbin Antony na Brazil.

A kakar bana Kubo ya ci kwallo shida ya kuma bayar aka ci uku a gasar La Liga. (Sun)

Kungiyoyin Jamus Bayer Leverkusen, da RB Leipzig da Stuttgart na neman sayen Jadon Sanch na Manchester United. (90 Min)

Watakila Juventus ta samu dama a kan Newcastle United a gogayyar da suke yi ta neman sayen Kalvin Phillips na Manchester City, wanda yake son ya san yadda za a rinka sanya shi a wasa a duk wata kungiya da za ta saye shi kafin ya yarda ya tafi can. Kuma na ganin zai fi samun damar taka leda sosai a Italiya. (Telegraph)

Brentford, da Brighton da kuma Nottingham Forest na sha'awar matashin dan wasan gaba na Hoffenheim, Maximilian Beier mai shekara 21, wanda yake tawagar Jamus ta 'yan kasa da shekara 21. Liverpool da Bayer Leverkusen ma na sa rai a kan matashin. (Christian Falk on X)

Chelsea ba ta da sha'awar sayen mai tsaron ragar Arsenal Aaron Ramsdale, dan Ingila a watan Janairu. Rahotanni na nuna cewa Ramsdale zai bar Emirates kasancewar wasa biyar aka fara sanya shi a kakar Premier ta bana. (Fabrizio Romano on X)

Sai dai kuma wasu bayanai na nuna cewa kungiyar ba za ta rabu da golan dan Ingila ba, a watan Janairu duk da rashin sa shi a wasa sosai. (Football Insider)

Everton ta tsuga kudin da ba ta taba sayar da wani dan wasa ba har fam miliyan 100 a kan matashin dan bayanta na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 Jarrad Branthwaite, yayin da Manchester United da Tottenham ke nuna sha'awarsu a kan matashin. (i newspaper)

Matashin dan wasan tsakiya na kungiyar Fluminense ta Brazil Andre, mai shekara 22, ya jaddada sha'awarsa ta wasa a gasar Premier yayin da Fulham ke nuna sha'awarta a kansa. (Standard)

Watakila Tottenham wadda ta dade tana sha'awar dan bayan Fulham Tosin Adarabioyo, ta nemi sayensa a watan Janairu, amma kuma ana ganin kila Fulham din ta tsawaita kwantiragin dan Ingilan har zuwa bayan bazara mai zuwa. (Standard)

Haka kuma Tottenham din ta fara tattaunawar cinikin dan bayan kungiyar Nice Jean-Clair Todibo a watan Janairu, kuma ita ma Manchester United an ce tana son sayen dan bayan na Faransa. (Talksport)

Kociyan da Nottingham Forest ta kora ranar Talata Steve Cooper, na daga cikin wadanda ake ganin za a zaba domin maye gurbin Roy Hodgson, idan kociyan mai shekara 76 ya bar Crystal Palace. (Standard)