Forest ta naɗa Nuno Espirito sabon kociyanta

An wallafa

Nottingham Forest ta nada Nuno Espirito Santo sabon kociyanta kan yarjejeniyar kaka biyu, ya maye gurbin Steve Cooper.

An kori Cooper ranar Talata, bayan shekara biyu yana horar da Forest, wanda ya yi rashin nasara biyar daga wasa shida, bayan da kungiyar take ta17 a kasan teburin Premier League.

Nuno tsohon kociyan Wolverhampton da Tottenham, an kore shi daga aiki a Al Ittahad mai buga gasar Saudi Arabia a cikin watan Nuwamba.

Mai shekara 49, zai fara jan ragamar Forest a gasar Premier League da za ta karbi bakuncin Bournemouth ranar Asabar.

Nuno ya yi kaka hudu a Wolverhampton, wadda ya kai Premier League daga Championship, wanda a kakar farko kungiyar ta kare a mataki na bakwai, sannan ta kai quarter finals a Europa League

Bayan ya bar Molineux, ya karbi aikin horar daTottenham a 2021, amma an kore shi kasa da wata hudu, bayan rashin nasara biyar a karawa bakwai.

Ya koma Al-Ittihad a Yulin 2022, wanda ya ja ragamar kungiyar ta lashe kofin Saudi Arabia a bara, amma aka sallame shi a bana bayan wasa 12, sakamakon kasa taka rawar gani.

Wasa daya Forest ta ci daga 13 da hada maki takwas daga cikin karawar.

Ta samu maki daya daga wasa shida na baya, kuma yanzu tana ta 17 da tazarar maki biyar tsakaninta da 'yan ukun karshe.