Chelsea za ta dauki Balogun daga Arsenal, Al-Ittihad na harin Raphael Varane

An wallafa

Chelsea na da sha’awar daukar dan gaban Amurka Folarin Balogun, daga Arsenal, wanda ta taya shi a kan fam miliyan 50, yayin da ita ma Monaco ma ke sha’awar dan wasan, amma Inter Milan ta fasa daukarsa yanzu. (Sky Sports)

Kazalika Chelsea ta nuna sha’awarta a kann dan bayan Real Valladolid dan kasar Spaniya Ivan Fresneda, to amma dan wasan mai shekara 18 ya fi son komawa Barcelona. (Mail)

Chelsea kuma dai ta kusa kammala yarjejeniyar daukar mai tsaron raga Djordje Petrovic, a kan kudi fam miliyan 11.8. (Evening Standard)

Manchester City na da yakinin cewa dan gefen Portugal Bernardo Silva, mai shekara 29, zai sanya hannu kan sabuwar kwantiragi da kungiyar duk da jita jitar da ake a kan makomarsa a kakar bana. (90 min)

Har yanzu Fiorentina ba ta karbi wani ta yi daga Manchester United a kan dan tsakiyar Morocco Sofyan Amrabat ba. . (Mirror)

Barcelona ta yi nisa a tattaunawa da Manchester City wajen daukar dan wasan Portugal Joao Cancelo, mai shekara 29, kuma dan wasan shi ma na son komawa can din. (Fabrizio Romano)

Luton ta yi tambaya a kan aron dan bayan Tottenham Japhet Tanganga, mai shekara 24. (Athletic - subscription required)

Kungiyar Al-Ittihad ta Saudiyya na harin dan bayan Manchester United dan kasar Faransa Raphael Varane, mai shekara 30. (Express)

An yi wa Paris St-Germain tayin dan gaban Barcelona dan kasar Spaniya Ansu Fati, mai shekara 20, wanda a baya ake gani zai koma Manchester United ko Arsenal. (Sun)

Dan wasan Bayern Munich Benjamin Pavard, mai shekara 27, ya zama daya daga cikin wadanda Inter Milan ke hari, yayin da Arsenal kuma ke nuna sha’awarta a kan dan wasan. (Evening Standard)

Kocin West Ham David Moyes, ya musanta cewa a yanzu yana son dauko Jesse Lingard, mai shekara 30 wanda tsohon dan wasan kungiyar ne a kan aro. (Mail)

Southampton na sha’awar daukar dan tsakiyar Jamus Luca Kerber, mai shekara 21, daga Saarbrucken. (Mail)