Chelsea ta ɗauki Romeo Lavia kan fam miliyan 58

An wallafa

Chelsea ta kammala sayen ɗan wasan tsakiyar Belgium Romeo Lavia daga Southampton kan kuɗi fam miliyan 53 tashin farko.

Dan wasan mai shekaru 19 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru bakwai a yarjejeniyar wanda zai iya tashi da ƙarin £5m.

Lavia ya buga wasanni 34 a dukkan gasa a kakar wasan da ta gabata amma ta kasa taimaka wa wajen hana Saints rikitowa daga gasar Premier zuwa matakin Championship.

Liverpool ta yi sha'awar Lavia, amma Southampton ta ki amincewa da tayin kusan fam milaya 46 da ta yi farkon wannan watan.

Lavia ya zama dan wasa na biyu a cikin wannan makon da ya zabi Chelsea a maimakon tawagar Jurgen Klopp, bayan Moises Caicedo, wanda ya koma Blues daga Brighton kan jimillar kuɗi fam miliyan 115.