Harry Maguire ya watsa wa Inter Milan kasa a ido, Liverpool na son sayen Kante

.
Bayanan hoto, Harry Maguire
An wallafa

Arsenal na duba yiwuwar sayen Jorginho, dan wasan tsakiyar Italiya mai shekara 31 ganin yadda kwantiraginsa da Chelsea ke gab da karewa. (Football London)

Paris St-Germain na fatan sayen Hakim Ziyech dan Morocco da ke bugawa Chelsea kwallo a matsayin aro zuwa karshen kakar bana kasancewar dan wasan mai shekara 29 na nuna sha'awar komawa Faransa a maimakon bugawa wata kungiya a Ingila. (L'Equipe)

Arsenal na tunanin taya dan wasan tsakiya na Leicester Youri Tielemans. Kwanitiragin dan wasan na Belgium mai shekara 25 za ta cika a karshen bazara amma Gunners na son habaka yan wasanta ba tare da bata lokaci ba. (90min)

Kyaptin din Manchester United Harry Maguire, 29, ya yi watsi da tayin Inter Milan da ke son daukarsa a matsayin aro domin tabbatar da matsayinsa a Old Trafford. (Daily Star)

Tottenham na gab da kammala kulla yarjejeniyar sayen Pedro Porro, mai shekara 23 kan £39.5m daga Sporting Lisbon(Telegraph - subscription required)

Sporting Lisbon za ta maye gurbin Porro da Hector Bellerin, 27, daga Barcelona(Fabrizio Romano)

Liverpool na iya daukan matakin bazata wajen sayen dan wasan Chelsea da Faransa N'Golo Kante, 31, wanda kwantiraginsa zai kare a Stamford Bridge a wannan bazarar. (El Nacional - in Spanish)

Southampton ta amince ta biya £26.2million domin sayen dan wasan gaba na Braga Vitinha, 22, wanda kuma ya taka leda a kungiyar kwalllon kafa ta Portugal yan kasa da shekara 21. (Football Insider)

Newcastle na hangen dan wasan Sheffield United da Norway Sander Berge, 24, a matsayin wanda zai iya maye gurbin Jonjo Shelvey, 30, wanda ke dab da komawa kungiyar Nottingham Forest (Newcastle Chronicle)

Nottingham Forest na gab da kulla yarjejeniya da dan wasan Atletico Madrid Felipe, 33, ganin yadda ba ya cikin jerin yan wasan da Diego Simeone ya bayyana za su buga wasa a kakar bana. (Mail)

Leicester ta gabatar da tayin £15m kan dan wasan Stoke da Australia Harry Souttar, mai shekara 24. Har ila yau, Foxes na sha'awar dan wasan Leeds Jack Harrison, mai shekara 26, amma dan wasan baya na Denmark Jannik Vestergaard, mai shekara 30, da Caglar Soyuncu, mai shekara 26 suna nan a kasuwa. (Telegraph - subscription required)

Dan wasan gaba na Manchester United Charlie McNeill, 19, yana tattaunawa domin komawa Newport County a matsayin aro, yayin da dan wasan baya mai 22- Di'Shon Bernard ke tattaunawa a kan koma wa Portsmouth(Mail)