Ko sauran ƙasashe za su iya shiga yaƙin Gaza da Isra'ila?

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK
Har yanzu duniya na cikin jimami na harin ban-mamaki da ƙungiyar Hamas ta kai cikin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, da kuma hare-haren ramuwar gayya da Isra'ila ke kaiwa a Zirin Gaza.
Ɗaruruwan ma'abota BBC sun turo tambayoyinsu game da rikicin, da irin tasirinsa, da abin da zai biyo baya, inda wasu ke tunanin ko wasu ƙasashe za su iya tsunduma cikin yaƙin.
Marubutanmu, waɗanda da yawansu suke kusa da filin yaƙin, sun amsa manyan tambayoyi biyu waɗanda aka fi neman amsarsu.
Ko yaƙin duniya na uku ne ke tafe?

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK
Craig Johnson mazaunin Skelmersal da ke Birtaniya ya tambaya cewa: Idan Iran ta shiga yaƙin kai-tsaye, hakan zai sa Amurka da ƙawayenta su ma su shiga?
Editan BBC na harkokin ƙasashen duniya Jeremy Bowen da ke kudancin Isra'ila ya amsa tambayar:
Lokacin da aka tambayi Shugaban Amurka Joe Biden kan yiwuwar Iran ko ƙungiyar Hezbollah su shiga yaƙin, sai ya ce: "Kada ku shiga wannan yaƙin."
Tuni Amurka ta tura jiragen ruwanta na yaƙi biyu zuwa gabashin Tekun Baharrum don aika saƙo mai ƙarfi ga Iran na cewa "kada ku shiga yaƙin nan".
Amurkar ta ce duk wanda ya shiga wannan yaƙi zai fuskanci sojojin ƙasar a filin dagar. Babban siyasar Gabas ta Tsakiya ita ce tsakanin Amurka da ƙawayenta, da kuma Iran da ƙawayenta.
Dukkan ɓangarorin na sane da irin haɗarin da ke gabansu.
Idan lamarin ya sauya daga cacar-baki zuwa fafatwa, zai karkatar da hankalin duniya kacokam zuwa Gabas ta Tsakiya.
Me ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta hana hare-haren da ake kai wa Gaza?

Asalin hoton, getty images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sadul Haq mazaunin birnin Landan ya yi tambaya: Idan kowa ya maince cewa Isra'ila na kashe fararen hula kuma za ta ci gaba da kashe wasu a Gaza, to me ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙasashe ba su hana ta ba?
Wakilin BBC kan harkokin diflomasiyya James Landale ya amsa:
Dalilin da ya sa ƙasashe ba su nemi Isra'ila ta dakatar da hare-hare ba saboda sun yarda cewa ita aka fara kai wa hari kuma tana da haƙƙin kare kanta.
Game da kiraye-kirayen a tsagaita wuta kuma, ya danganta ne da yadda Isra'ilar ke kare kan ta.
Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya faɗa ranar Litinin cewa sun yi magana da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, inda ya faɗa masa buƙatar "kare fararen hula".
Ita ma Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta nemi Isra'ilar ta guji kai wa fararen hula hari.
Babban Sakataren MDD Antonio Guterres ya faɗa 'yan kwanaki da suka wuce cewa: "Wajibi ne a kiyaye dokokin ƙasashen duniya game da haƙƙin ɗan'adam, dole ne a kare rayukan fararen hula kuma kada a yi amfani da su a matsayin garkuwa daga yaƙi."
Isra'ila ta haƙiƙance cewa jiragenta da makamai na yin luguden wuta ne a kan Hamas da ke Gaza. Amma tuni ta kashe fararen hula da yawa tare da jikkata wasu da dama.
Falasɗinawa na cewa dalilin da ya sa ake kashe farar hula shi ne hare-haren na Isra'ila sun wuce gona da iri kuma babu tsari.
Ita kuma Isra'ila na cewa hakan na faruwa ne saboda Hamas na amfani da fararen hular a matsayin garkuwa daga yaƙi.














