Rasuwar Sarauniya Elizabeth II: Taswirar tsarin iyalan Sarautar Birtaniya a jere

An wallafa

Sarauniya Elizabeth ta biyu ita ce wacce ta fi daɗewa a tarihin sarautar Birtaniya.

Tana da ƴaƴa huɗu da jikoki takwas da tattaɓa-kunne 12.

Ta rasu ranar 8 ga watan Satumba bayan shafe shakera 70 a karagar mulki, inda babban ɗanta Charles, ya gaje ta.

Ga dai cikakkun bayanai kan yadda tsarin iyalan masarautar yake da kuma magadanta.

Sarauniya da Yarima Philip, Duke na Edinburgh

Sarauniya ce ta fi kowa daɗewa a gadon sarautar Birtania inda ta shafe shekara 70.

Ta rasu tana da shekara 96 ranar 8 ga Satumban 2022. Gimbiya Elizabeth wacce aka haifa a shekarar 1926, ta zama Sarauniya ne bayan mutuwar mahaifinta Sarki George VI a 1952.

Ta auri Philip, Duke na Edinburgh, a shekarar 1947 kuma ma'auratan suna da ƴaƴa huɗu da suka haɗa da Charles da Anne da Andrew da kuma Edward.

An haifi Yarima Philip wanda tsohon ɗan sarki ne a Denmark da Girka, a shekarar 1921 kuma ya yi aiki a matsayin sojan ruwan Birtaniya lokacin yaƙin duniya na biyu.

Shi ne mijin sarauniya mafi daɗewa a gadon sarautar Birtaniya, ya kuma yi murabus daga jan ragamar abubuwan da suka shafi masarauta a shekarar 2017 bayan kammala ayyukan da suka hau kansa fiye da 22,000.

Ya rasu a watan Afrilun 2021.

Jerin magada - Charles ya zama Sarki

An haife shi a shekarar 1948

Babban ɗan Sarauniya ya zama shi ne sabon Sarki Charles na uku.

Tsohon Yariman Wales ɗin ya taɓa auren Diana Spencer, wadda ta zama Gimbiyar Wales ranar 29 ga Yulin 1981.

Ma'auratan na da ƴaƴa maza biyu, William da Harry.

Daga baya sun rabu aurensu ya mutu a 1996.

Ranar 31 ga Augustan 1997 kuma, gimbiyar ta mutu a wani hatsarin mota a Paris.

Ya auri Camilla Parker Bowles ranar 9 ga Afrilun 2005.

1. Yarima William, Duke na Cornwall da Cambridge

An haife shi a shekarar 1982

Yarima William shi ne babban ɗan sabon Sarki Charles na uku da ya Diana, Gimbiyar Wales, kuma a yanzu shi ne na farko a layin masu bjiran gadon masarautar.

Duke na da shekara 15 lokacin da mahaifiyarsa Diana ta rasu. Ya yi karatu a Jami'ar St Andrews inda ya haɗu da matar da ya aura, Kate Middleton.

Sun yi aure a shekarar 2011. A lokacin da ya cika shekara 21 aka naɗa shi babban mai hidima na gwamnati ga Sarauniya.

Shi da matarsa sun haifi ɗansu na farko George a watan Yulin 2013, ta biyun Charlotte, a 2015 da na ukun Louis a 2018.

Yarima ya samu horo a rundunar sojin ƙasa da rundunar sojin ruwa kafin ya shafe shekara uku a matsayin matuƙin jirgin rundunar sojin sama a arewacin Wales.

Ya kuma yi aikin wucin gadi na shekara biyu a matsayin matukin jirgin sama a kamfanin jirage na East Anglian da kuma yin wasu aikace-aikacensa na gidan sarauta.

Ya bar aikin a watan Yulin 2017 domin ci gaba da ayyukansa na gidan sarauta a madadin sarauniya da kuma Duke na Edinburgh.

A matsayinsa na Yarima mai jiran gadon sarauta, babban aikinsa shi ne taimaka wa Sarki a wasu hidimominsa na sarauta.

2. Yarima George na Cornwall da Cambridge

An haife shi a shekarar 2013

An haifi Yarima George na Cornwall da Cambridge ranar 22 ga watan Yulin 2013 a asibitin St Mary da ke birnin Landan.

A kan idon Yarima William aka haifi dansa George.

Yarima George shi ne na biyu a jerin masu gadon sarautar Birtaniya bayan mahaifinsa.

3. Sarauniya Charlotte ta Cornwall da Cambridge

An haife ta a shekarar 2015

Duchess ta Cornwall da Cambridge ta haifi danta na biyu wacce ta kasance mace, a ranar 2 ga watan Mayun 2015 a asibitin St Mary.

Shi ma Duke na Cornwall yana nan lokacin da aka haifi 'yar tasa. Duke din da kuma Duchess sun saka mata suna Charlotte Elizabeth Diana.

Ita ce ta hudu a jerin masu gadon sarautar Birtaniya bayan mahaifinta da kuma babban wanta, an kuma fi saninta da Sarauniya Charlotte ta Cornwall da Cambridge.

4. Yarima Louis na Cornwall da Cambridge

An haife shi a shekarar 2018

Duchess ta Cornwall da Cabridge ta haifi danta na uku a ranar 23 ga watan Afrilun 2018, a asibitin St Mary da ke Landan.

A kan idon Duke aka haifi Louis Arthur Charles, wanda shi ne na hudu a jerin gadon sarautar Birtaniya.

5. Yarima Harry, Duke na Sussex

An haife shi a shekarar 1984

Yarima Harry ya samu horo a makarantar horar da sojoji na gidan sarauta da ke Sandhurst, inda ya kuma samu damar zama laftanar a rundunar soji da kasance a matsayin matukin jirgin sama.

A tsawon shekaru goma da ya yi a rundunar sojoji, Kaftin Wales, kamar yadda aka fi saninsa, ya yi aiki na kwarai a Afghanistan har sau biyu, a shekarun 2012 da 2013 a matsayin mai harbin bindiga da kuma matukin jirgin sama.

Ya bar rundunar sojojin a 2015 inda ya maida hankali wajen yin ayyukan agaji da suka hada da kula da gandun a Afirka da shirya wasanni ga mambobin rundunar soji da suka samu raunuka.

Ya kaance babban mai taimakawa sarauniya kan hidimomin sarauta tun bayan bikin cika shekara 21 na haihuwarsa, inda ya rika tayata aiki a wasu ayyukanta.

Ya auri wata 'yar fim yar Amurka Meghan Markle ranar 19 ga watan Mayun 2018 a fadar Windsor.

A watan Janairun 2020, ma'auratan 'yan gidan sarauta sun ce za su yi baya a matsayin manyan 'yan gidan sarauta inda suka rika yin rayuwa tsakanin Birtaniya da Arewacin Amurka.

Sun ce sun yi hakan ne domin yin aiki da kuma dogaro da kansu.

Shekara daya bayan nan, fadar Buckingham ta tabbatar da cewa ma'auratan ba za su koma yin ayyuka a gidan sarauta, inda kuma za su ajiye girmamawa da aka basu ta rundunar soji da na gidan sarauta.

6. Archie Harrison Mountbatten-Windsor

An haife ta a shekarar 2019

An haifi yaron sussexes na farko Harrison Mountbatten-Windsor a ranar 6 ga watan Mayun 2019,

Bayan rada masa suna, ma'auratan sun zabi kin sanya wani suna na daban da za a rika kiran da nasu.

Lokacin da aka sanar da sunan, wakilin BBC na gidan sarauta, Jonny Dymond ya ce matakin ya nuna cewa ma'auratan basa son girmar da shi a matsayin dan gidan sarauta.

7. Lilibet Diana Mountbatten-Windsor

An haife ta a shekarar 2021

Duchess na Sussex ta haifi 'yar ta ta farko a ranar 4 ga watan Yunin 2021, a Santa Barbara.

An fi sanin Lilibet Diana Mountbatten-Windsor - da Lili - wadda kuma suna ne na gidan sarauta na Sarauniya kuma ita ce tattaba-kunne ta 11 ga Sarauniyar.

An sanya mata sunan Diana domin girmama mahaifiyar Yarima Harry, wacce ta rasu a wani hadarin mota a shekarar 1997, tana kuma da shekara 12 a lokacin.

8. Duke na York

An haife shi ne a shekarar 1960

Yarima Andrew, wanda ya kasance na takwas a jerin magada sarautar Birtaniya, shi ne yaro na uku a wajen Sarauniya da Duke na Edinburgh - amma shi ne na farko da aka haifa a gidan sarauta cikin shekara 103.

An ba shi Duke na York a ranar aurensa da Sarah Ferguson, wacce ta zama Duchess ta York, a 1986.

Suna da 'ya'ya mata biyu - Beatrice wacce aka haifa a 1988, sai kuma Eugene a 1990. A watan Maris din 1992 , an sanar cewa Duke da Duchess din za su rabu.

Auren su ya mutu a 1996. Duke din ya yi aiki da rundunar sojin ruwa ta gidan sarauta na tsawon shekara 22, inda kuma aka yi yakin Falkland ta 1982 tare da shi.

Dadin dadawa ga sarautan ayyukan gidan sarauta, ya kasance a matsayin wakili na musamman kan harkokin kasuwanci ga gwamnatin har zuwa 2011.

Yarima Andrew ya ja baya da yin ayyukan gidan sarauta a 2019 bayan wata tattaunawa da BBC kan dangantakarsa da Jerry Epstein, wanda ya kashe kansa lokacin da yake jiran hukunci kan zargin safarar 'yan mata domin yin lalata da su da kuma laifuka hada baki da shi.

A watan Febrairu, ya amince da biyan wasu kudade da ba a bayyana ba domin kashe maganar laifin cin zarafi da ake tuhumarsa a Amurka, duk da cewa ya musanta zargin.

9. sarauniya Beatrice

An haife ta a shekarar 1988

Sarauniya Beatrice, ita ce diyar Yarima Andrew da Sarah, Duchess a York.

Asalin sunanta shi ne Sarauniya Beatrice ta York. Babu wani suna da ake kiranta face wannan, amma tana amfani da York.

Ta auri wani hamshakin mai gudanar da harkokin kayayyaki Edoardo Mapelli Mozzi a cocin St Royal Lodge da ke Windsor a watan Yulin 2020.

An shirya gudanar da aure ne tun a watan Mayu, sai dai cutar korona ta sa an jinkirta shirye-shiryen bikin.

10. Sienna Elizabeth Mapelli Mozzi

An haife ta a shekarar 2021

Sarauniya Beatrice ta haifi 'yar ta mai suna Sienna Elizabeth a watan Satumban 2021, wadda kuma shine na 10 a jerin masu gadon sarautar Birtaniya, kuma shi ne tattaba-kunne na 12 ga Sarauniya.

Sarauniya Beatrice, ita ce kuma matar dan mista Mapelli Mozzi Christopher Woolf wanda aka fi sani da Wolfie, a dangantakarsa ta baya da Dara Huang.

11. Sarauniya Eugenie

A haife ta ne a shekarar 1990

Sarauniya Eugenie, ita ce yar Yarima Andrew da sarah Duchess na York.

Asalin sunanta shi ne Sarauniya Eugenie na York, kuma na 11 a jerin masu gadon sarautar Birtaniya.

Kamar 'yar uwarta Sarauniya Beatrice, babu wani suna na biyu da ake kiranta da shi, amma tana amfani da York.

Ta auri saurayinta da suka dade suna soyayya Jack Broosbank a fadar Windsor , ranar 12 ga watan Oktoban 2018.

12. August Philip Hawke Brooksbank

An haife shi a shekara ta 2021

Sarauniya Eugenie da Jack Brooksbank, sun haifi dan su mai suna August, ranar 9 ga watan febrairun 2021, kuma shi ne tattaba-kunne a 9 ga Sarauniya Elizabeth.

13. Earl na Wessex

An haife shi a shekara 1964

An baiwa Yarima Edward mukamin Earl na Wessex da Viscount Severn a ranar aurensa da Sophie Rhys-Jones a 2007.

Ma'auratan na da 'ya'ya biyu, Lady Louse wacce aka haifa a 2003 a kuma James Viscount Severn a 2007.

Bayan wani lokaci a gidan sarauta, yariman ya kafa wani kamfanin talabijin.

A yanzu, yana taimaka wa Sarauniyar da wasu ayyuka inda kuma yake gudanar da aikin bada agaji. Shi ne a 13 a jerin masu gadon sarautar Birtaniya.

14. James, Viscount Severn

An haife shi a shekarar 2007

Viscount Severn, shi ne karamin da ga Earl da Countess na Wessex.

Ma'auratan sun dauki matakin rika kiran 'ya'yan nasu da Earl maimakon yarima ko sarauniya.

An bayyana cewa sun dauki matakin haka ne saboda cire musu dawainiya ta sarauta.

15. Lady Louise

An haife ta a shekarar 2003

An haifi Lady Louise a shekarar 2003 a Widsor, ta kuma kasance babar diya ga Earl da Countess na Wessex.

Sai dai, tana kasa a jerin masu gadon sarautar Birtaniya idan aka kwatanta da kaninta saboda an haife ta ne kafin wata dokar da ta nuna namiji zai iya fin samun dama sama da mace a masu son gadon sarautar.

16. Sarauniya Royal

An haife ta a shekarar 1950

Anne, da ake kira sarauniya Royal, ita ce 'ya ta biyu kuma mace daya tilo da sarauniya.

Tana jeri na uku a masu gadon sarautar Birtaniya lokacin da aka haife ta, amma a yanzu tana jeri na 16.

An bata mukamin Sarauniya Royal ne a watan Yunin 1987. Sarauniya Anne ta taba aure har sau biyu; Mijinta na farko kaftin Mark Phillip, shi ne mahaifin 'ya'yanta guda biyu Peter da Zara, yayin da mijinta na biyu ya kasance Vice-Admiral Timothy Laurence.

Sarauniyar ita ce ta farko a gidan sarauta da ta fara amfani da sunan Mountbatten-Windsor a cikin wani kundin rajista na aurenta da kaftin Phillips.

17. Peter Phillips

An haife shi a shekarar 1977

Peter Phillips shi ne babban da jika ta Sarauniya Elizabeth.

Ya auri Kelly a 2008, kuma sun haifi 'ya'ya mata guda biyu Savannah a 2010 da kuma Isla a 2012.

'Yaran sarauniya Royal basu da wani suna na gidan sarauta da ake kiransu da shi saboda suna jerin mata.

Peter Phillips da matarsa sun sanar da cewa za su rabu a watan Febrairun 2020.

18. Savannah Phillips

An haife ta a shekarar 2010

An haifi Savannah a 2010, ta kuma kasance babbar 'ya ga Peter da Autumn Phillips. Ita ce kuma tattaba-kunne ta farko ga Sarauiya Elizabeth.

19. Isla Phillips

An haife ta a shekarar 2012

An haifi Isla, a 2010. ita ce 'ya ta biyu ga Peter da Autumn Phillips.

20. Zara Tindall

An haife ta a shekarar 1981

Zara Tindall ta bi sahun mahaifanta wajen iya tuki - wanda har ya sa ta samu lambar yabo a gasar Olympics na 2012 da aka gudanar a birnin Landan.

Ta auri wani tsohon dan wasan zari-ruga na dan kasar Ingila Mike Tindall a 2011, kuma sun haifi 'yar su ta farko mai suna Mia Grace a 2014.

Ta kasance na 20 a jerin masu gadon sarautar Birtaniya.

21. Mia Grace Tindall

An haife ta a shekarar 2014

Zara Tindall, wacce ta kasance tattaba-kunne ga Sarauniya Elizabeth, ta haifi 'yar ta ta farko, Mia Grace a watan Janairun 2014.

22. Lena Elizabeth Tindall

An haife ta a shekarar 2018

A haifi Lena Elizabeth ne ranar 18 ga watan Yunin 2018 a asibitin Stroud da ke Gloucestershire.

An sanaya mata sunan ne domin girmama kakar ta.

Lena , kamar 'yar uwarta, bata da wani suna da ake kiranta na gidan sarauta don haka za a kuma rika kiranta da Miss Tindall.

23. Lucas Philip Tindall

An haife ta a shekarar 2021

A haifi Lucas Philip da ya zamo da na uku ga Zara da Mike Tindall - wadda kuma ya kasance tattaba-kunne na 10 ga Sarauniya Elizabeth, a ranar 21 ga watan Maris din 2021.