Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tuchel zai bar Bayern duk da cewa magoya baya na son ya tsaya
Kocin Bayern Munich Thomas Tuchel ya tabbatar zai bar kungiyar a karshen wannan kakar, duk da cewa yana tattaunawa da kungiyar kan ko zai ci gaba da zama.
A atan Fabirairu ne aka sanar da cewa kocin dan kasar Jamus mai shekara 50 zai bar kungiyar yayin da yake da shekara guda da ta rage masa a kwataraginsa, wannan kakar dai mai wahala ce ga Bayern, kuma Leverkusen ta lashe Bundesliga.
An samu korafe-korafe daga magoya baya na neman Tuchel ya ci gaba da tsayawa a kungiyar, sai dai tsohon kocin na Chelsea ya ce "ba a cimma yarjejeniya ba kan maganar".
"Har yanzu yarjejeniyar da muka cimma a watan Fabirairu ce a hannu", in ji Tochel da ya karbi aikin Bayern a watan Maris din 2023.
Wasan karshe da Tochel zai jagoranta a matsayin kocin Bayern shi ne wanda za su je Hoffenheim a ranar Asabar, kuma shi ne wasan kungiyar na karshe a wannan kakar.
Bayan an sanar da zai bar kungiyar, Bayern ta doke Arsenal a wasan kusa da daf da na karshe a Champions sai kuma Real Madrid ta koreta daga gasar a wasan kusa da na karshe.
Bayern na ta fadi tashin yadda za ta maye gurbin Tuchel tun a watan Fabirairu, kuma tun daga nan ake yada labaran cewa Manchester United Na neman maye gurbin Erik ten Hag da shi. Ko da yake itama Bayern na neman Ten Hag din.
Nasarar da Leverkusen ta samu ta lashe Bundesliga ya kawo karshen lashe kofin da Bayen ta yi na shekara 11 a jere.