Lewandowski ne kan gaba a cin ƙwallaye a La Ligar bana

Robert Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Robert Lewandowski ne kan gaba a cin ƙwallaye a gasar La Liga, bayan da aka kammala karawar sati na tara a karshen mako.

Ranar Lahadi Barcelona ta je ta doke Deportivo Alaves 3-0, kuwa Lewandowski ne ya zura uku rigis a raga.

Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburi da maki 24, bayan wasa tara da yin nasara takwas aka doke ta karawa ɗaya.

Haka kuma Barcelona ta zura ƙwallo 28, ita kuma aka zura mata tara a raga a babbar gasar tamaula ta Sifaniya. bayan fafatawa tara.

Kawo yanzu Lewandoeski ya ci ƙwallo 10 a wasa tara da fara kakar nan daga 28 da Barcelona ta zazzaga a raga a bana.

Wanda yake biye da Lewandowski shi ne Perez na Villareal, wanda ya ci shida, sai Mbappe na Real Madrid da Celso na Betis da Raphinha na Barcelona da kowanne keda biyar.

Barcelona za ta buga wasa uku nan gaba masu zafi, wadda za karɓi baƙuncin Sevilla a wasan mako na 10 a La Liga ranar Lahadi 20 ga watan nan Oktoba.

Daga nan Barcelona za ta je Bayern Munich domin karawa a Champions League ranar 23 ga watan Oktoba.

Wasa na uku da Barcelona za ta yi shi ne wanda za ta ziyarci Real Madrid a wasan hamayya na El Clasico ranar Asabar 26 ga watan Oktoba.

Wasa uku da ke gaban Barcelona:

Liga Lahadi 20 Oktoba

  • Barcelona da Sevilla

Champions League Laraba 23 ga watan Oktoba

  • Barcelona da Bayern Munich

Liga Asabar 26 ga waan Oktoba

  • Real Madrid da Barcelona

Jerin waɗanda ke kan gaba a cin ƙwallaye a La Liga:

  • R. Lewandowski Barcelona 10 28
  • A. Pérez Villarreal 6 17
  • K. Mbappé R. Madrid 5 19
  • G. L. Celso R. Betis 5 8
  • Raphinha Barcelona 5 28
  • V. Júnior R. Madrid 4 19
  • O. Sancet A. Club 4 13
  • I. Aspas C. Vigo 4 16
  • B. Iglesias C. Vigo 4 16
  • L. Yamal Barcelona 4