Za a binciki Lamine Yamal kan bikin cika shekara 18

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Spain za su gudanar da bincike kan ɗanwasan gaba na Barcelona Lamine Yamal bayan rahotannin cewa ya gayyato wadanni a wajen bikin murnar cika shekara 18 da haihuwa.
Ma'aikatar kare haƙƙin al'umma a Spain ce ta buƙaci ofishin babban mai gabatar da ƙara ya gudanar da bincike kan ɗanwasan.
Lamine Yamal ya gudanar da bikin ne a ranar Lahadi a wani gidan da ya karɓi haya a garin Olivella da ke kusa da Barcelona, inda ya gayyato baƙi da dama da suka haɗa da abokan wasansa da waɗanda suka yi fice a YouTube da kafofin sada zumunta na Intanet.
Ana zargin Lamine Yamal da ɗauko hayar wadanni domin nishaɗantar da baƙinsa, wani abin da ƙungiyar da ke kare su ta ce "ba za a amince ba a wannan ƙarni na 21."
Rahotanni sun ce har ƙungiyar ta ADEE ta shigar da ƙara.
Amma hukumomin Spain sun ce za a gudanar da bincike ne domin tabbatar da ko ɗanwasan ya saɓa doka da kuma saɓa ƴancin masu buƙata ta musamman.
Barcelona dai ba ta ce komi ba game da zargin da ake yi wa ɗanwasanta, amma ta ce za ta yi nata bincike





