Kafar Arsenal ɗaya ta kai ƙwata fainal a Champions League

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

PSV Eindhoven ta sha kashi a hannun Arsenal da cin 7-1 a wasan farko zagayen ƴan 16 a Champions League da suka kara ranar Talata a Netherlands.

Gunners ta ci ƙwallayen ta hannun Timber da Nwaneri da Mikel Merino da kuma ƙyaftin, Odegaard mai biyu a raga.

Sauran da suka ci wa Gunners ƙwallayen sun haɗa da Trossard da kuma Calafiori, yayin da PSV ta zare ɗaya ta hannunn Lang a bugun fenariri.

Wannan shi ne wasa na 11 da suka kara tsakanin PSV da Arsenal a gasar zakarun Turai, Gunners ta yi nasara biyar da canjaras huɗu, PSV ta yi nasara biyu.

Arsenal za ta karɓi bakuncin wasa na biyu a gasar zakarun Turai ranar Laraba 12 ga watan Maris a Emirates.

Sai dai kafin nan Gunners za ta je gidan Manchester United a wasan mako na 28 a Premier League a Old Trafford.

Haka kuma Arsenal za ta kece raini da Chelsea a Emirates a Premier League ranar Lahadi 16 ga watan Maris.