Man United na mutuwar son ɗaukar Vinicius Jr, Sané zai iya komawa Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
Ruben Amorim yana son daukar Ousmane Diomande zuwa Manchester United, Batun halin da fitaccen dan wasan Turai Vinicius Jr ke ciki, kocin Wolves Gary O'Neil na fuskantar matsin lamba.
Ruben Amorim na son dauko dan wasan bayan Sporting na Ivory Coast, mai shekara 20, Ousmane Diomande, wanda aka kiyasta a kan fan miliyan 70, zuwa Manchester United. (Sun)
Har yanzu Arsenal na zawarcin dan wasan gaban Sporting na Sweden Viktor Gyokeres wanda yanzu haka ke duba yiwuwar tashi bayan tafiyar Amorim. (TeamTalk)
Sai dai Manchester United za ta iya yin gogayya da abokan hamayyarta na Premier Arsenal da Chelsea da Liverpool da kuma Manchester City a yunkurin sayen Gyokeres. (Florian Plettenberg)
Manchester United na ta kokarin bibiya da kuma fadi tashi wajen zawarcin dan wasan gaban Real Madrid Vinicius Jr, mai shekara 24, yayin da ake tattauna batun kwantiraginsa na Yuro biliyan daya. (Relevo TeamTalk)
Tsohon dan wasan Liverpool da Ingila Steven Gerrard ya sha alwashin ci gaba da zama kocin Al-Ettifaq bayan kiraye kirayen ya yi murabus daga mukamin. (Mail)
Yan wasan Manchester United na neman kocin rikon kwarya na kasar Holland Ruud van Nistelrooy ya ci gaba da zama a kungiyar bayan da Amorim ya karbi ragamar horar da kungiyar ta Old Trafford. (Sun)
Kocin Arsenal Mikel Arteta na son dauko dan wasan Bayern Munich Leroy Sane, mai shekara 28. (Christian Falk, Bild)
Gunners da Southampton takwararta ta Premier suna sha'awar sayen dan wasan gaban Palmeiras dan kasar Brazil mai shekara 18, Luighi. (Nosso Palmeiras)
Kocin Chelsea Enzo Maresca zai iya fuskantar babban kalubale idan yana son dakko dan wasan bayan Denmark mai shekaru 20 Patrick Dorgu zuwa Stamford Bridge, yayin da tauraron na Lecce ke shirin ci gaba da kasancewa a Seria A. (GiveMeSport)
Kocin Wolves Gary O'Neil yana da wasanni biyu kacal domin ya ceci aikinsa bayan da suka fara rashin nasara a kakar wasa ta bana. (Football Insider}
Tottenham ce ke kan gaba wajen neman dan wasan gaba dan kasar Ireland Mason Melia mai shekaru 17, wanda ke taka leda a kulob din St Patrick's Athletic da ke Dublin. (TeamTalk)
Kocin Inter Miami Gerardo Martino ya ce siyan Neymar daga Al-Hilal ba zai yuwu a halin yanzu ba, yayin da ake rade-radin dan wasan na Brazil mai shekara 32 zai iya komawa kungiyar ta MLS. (ESPN)











