‘Mutum ɗaya cikin huɗu da ke da ciwon suga ba su samun taimakon da ya dace’

Asalin hoton, Alexander Vasquez
Wani bincike wanda aka fitar da shi a ranar yaƙi da ciwon suga ta duniya ya bayyana cewa mutum ɗaya cikin huɗu a faɗin duniya da ke fama da ciwon suga ba su samun taimakon da suke buƙata.
Hukumar yaƙi da ciwon suga ta duniya ta bayyana cewa kusan kashi 26 cikin 100 na masu cutar ba su samu isassun bayanai ba kan halin da suke ciki a lokacin da aka gano suna da cutar wanda hakan zai iya sa su kasa kula da kansu.
Hakan zai iya jawo musu matsaloli kamar shanyewar rabin jiki da ciwon koda da makanta da kuma jawo matsala ga lafiyar ƙwaƙwalwa.
An gudanar da wannan bincike ne ta intanet ga mutum 3,208 waɗanda ko dai sun taɓa samun ciwon suga ko kuma malaman lafiya ne daga wasu ƙasashe kamar Brazil da India da Najeriya.
Amma ga wanda yake da ciwon suga, abubuwan da wannan binciken ya gano ba wani abin mamaki bane a gare ni, wani abu ne da na sani.
'An gano ina da ciwon suga amma ba ni da ilimi kan cutar'
Ganin cewa ina da ciwon suga nau'in Type 1, an gano ina da ciwon ina ɗan shekara bakwai a Costa Rica, zan iya danganta yadda na ji da wahalar da na sha a lokacin da nake girma ba tare da ina da wata masaniya ba kan abin da ke damu na.
An gano ina da ciwon suga kuma na same shi ne sakamakon irin illar da wani magani ya yi mani inda a lokacin ina da wani ciwon ƙashi wanda da keken guragu nake tafiya.
A lokacin da nake tasowa, lokacin da ba ni da na'urar auna sindarin glucose da ke jikina, ina yawan samun tashin hankali kada ciwona ya tashi inda wani lokaci nake mantuwa idan na yi allurar sukari ko na manta na yi sau biyu wanda hakan zai iya sa adadin sukarin da ke cikin jinina ya yi ƙasa kuma ya yi barazana ga rayuwata.
Bayan mun koma Birtaniya da zama lokacin ina da shekara 25, a lokacin ne na ƙara samun bayani a kan ciwon.
Amma a yau sakamakon irin ilimi da kuma kayayyaki da na samu daga hukumar lafiya ta Birtaniya NHS, ina jin dadi matuka sakamakon irin matakan da nake dauka a kullum domin na zauna lafiya saboda cutar da nake fama da ita.
Na yi magana da wata mai cutar domin sanin ko ta shiga irin halin da na shiga, inda na yi magana da Ana Lucia daga Chihuahua da ke Mexico.
Ta yi mani bayanin cewa bayan an gano tana da ciwon suga, rayuwa ta sauya mata matuƙa, ba wai gareta ba amma ga iyalanta.

Asalin hoton, Clementina
An gano Ana Lucia tana da ciwon suga nau'in Type 1 a lokacin da take shekara takwas da haihuwa bayan an kai ta sashen kula da marasa lafiya na musamman.
Mahaifiyarta, Clementina ta bayyana mana yadda ta ji sakamakon ba a masu bayanai sosai ba lokacin da ƴarta ta shafe kwana biyar a asibiti.
"Sun bayyana mani akwai buƙatar na koyi yadda zan yi mata allura saboda yarinya ce. A lokacin ne dukanmu muka soma samun ilimi kan ciwon suga.
Sai dai ƙarancin taimako da wayar da kai kan ciwon sukari ya yi tasiri matuƙa kan Clementina da ƴarta, a daidai lokacin da suke ƙoƙarin kawo sauyi ga halin da ake ciki.
Mece ce cutar ciwon sukari?
- Ciwon sukari cuta ce wadda ba ta da magani
- Ana samun ciwon ne idan jikin ɗan adam ba ya iya kula da adadin sukarin da ke cikin jiki.
- Akwai nau'o'i biyu na ciwon sukari, akwai Type I da Type II
Zuwa yanzu dai Ana Lucia ta shafe shekara 17 tana fama da matsalar ciwon na sukari, akasari kuma ita ke kula da kanta.
Duk da cewa ta bayyana mutum zai iya gajiya: "Ba na bacci sosai sakamakon ina yawan duba adadin sukarin da ke jinina ko kuma na jira bayan wasu sa'o'i domin na yi allura,"
Ba da daɗewa ba ta soma saka na'urar awon sindarin glucose wanda na'ura ce da ake amfani da ita ba sai ta huda yatsanta ba domin ɗibar jini ta yi awo.
Ta bayyana cewa da tun can dama tana da wannan na'urar da ta taimaka mata wurin kula da lafiyarta.
Duk da cewa ƴan uwa da abokan arziki na Lucia suna ba ta goyon bayan da ya kamata, amma tana ganin ƙalubalen da take fuskanta sakamakon makaranta da sauran wahalhalun yau da kullum ƙalubale ne gare mu
Tasiri kan lafiyar kwakwalwa

Asalin hoton, Getty Images
Binciken da aka yi kuma ya duba batun tasirin ciwon suga kan lafiyar ƙwaƙwalwa musamman idan mutum ba shi da ilimi sosai kan ciwon.
Shugaban hukumar yaƙi da ciwon suga ta duniya Farfesa Andrew Boulton ya bayyana cewa an gano idan mutum bai samu ilimi kan ciwon yadda ya kamata ba, hakan zai iya jawo damuwa da baƙin ciki.
Binciken da aka yi ya gano cewa akwai buƙatar su ma hukumomin lafiya a wayar musu da kai kuma rabin waɗanda aka yi bincike a kansu sun bayyana cewa sun gano damuwa na daga cikin abubuwan da ke ƙara ta'azzara ciwon suga.
"Mutanen da ke fama da damuwa, akwai yiwuwar ba za su iya bin shawarwarin likitoci ba...misali idan suna da matsala a ƙafa, kada su saka wasu takalma," in ji Farfesa Boulton










