An tsayar da ranar El Clasico tsakanin Barca da Real a La Liga

El Clasico

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

La Liga ta tsayar da ranar 19 ga watan Maris, domin buga El Clasico tsakanin Barcelona da Real Madrid wasan mako na 26 a Nou Camp.

Barcelona tana ta daya a kan teburin La Liga da maki 59 da tazarar maki takwas tsakani da Real Madrid ta biyu mai maki 51.

Ranar Asabar Real Madrid ta je ta ci Osasuna 2-0 a wasan mako na 22 a La Liga, ita kuwa Barcelona doke Cadiz 2-0 ta yi ranar Lahadi.

Robert Lewandowski na Barcelona shine kan gaba a yawan cin kwallaye a La Liga a bana, mai 15, Karim Benzema na Real Madrid 11 ya zura a raga, iri daya da yawan na Joselu na Espanyol.

Real Madrid ta doke Barcelona 3-1 a La Liga ranar 16 ga watan Oktoban 2022 a Santiago Bernabeu.

Barcelona ta dauki Spanish Super Cup a Saudi Arabia ranar 15 ga watan Janairun 2023, bayan cin Real Madrid 3-1 a karawar karshe.

Sai dai kungiyoyin za su fara fafatawa a El Clasico a Copa del Rey wasan farko na daf da karshe ranar 2 ga watan Maris a Santiago Bernabeu.

Daga nan za su fuskanci juna a wasa na biyu a La Liga a kakar nan.

Za kuma su kece raini a wasa na biyu na daf da karshe a Copa del Rey da za a yi a Camp Nou ranar 5 ga watan Afirilu.

Wasa shida da Barcelona za ta buga nan gaba:

Europa League Alhamis 23 ga Fabrairun 2023

  • Man Utd da Barcelona

Spanish La Liga Lahadi 26 ga Fabrairun 2023

  • Almeria da Barcelona

Copa del Rey wasan farko Alhamis 02 ga Maris 2023

  • Real Madrid da Barcelona

Spanish La Liga Lahadi 05 Maris 2023

  • Barcelona da Valencia

Spanish La Liga Lahadi 12 ga watan Maris 2023

  • Ath Bilbao da Barcelona

Spanish La Liga Lahadi 19 ga watan Maris 2023

  • Barcelona da Real Madrid

Wasa bakwai da Real Madrid za ta kara nan gaba:

Champions League Talata 21 ga Fabrairun 2023

  • Liverpool da Real Madrid

Spanish La Liga Asabar 25 ga Fabrairun 2023

  • Real Madrid da Atl Madrid

Copa del Rey wasan farko Alhamis 02 Maris 2023

  • Real Madrid da Barcelona

Spanish La Liga Lahadi 05 Maris 2023

  • Real Betis da Real Madrid

Spanish La Liga Asabar 11 ga Maris 2023

  • Real Madrid da Espanyol

Champions League Laraba 15 ga Maris 2023

  • Real Madrid da Liverpool

Spanish La Liga Lahadi 19 ga Maris 2023

  • Barcelona da Real Madrid