Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fadar shugaban kasa ta yi watsi da sukar Obasanjo kan dimokuraɗiyya
Mahukunta da masana harkokin siyasa a Najeriya, na cigaba da tofa albarkacin bakinsu game da wani furuci da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi cewa tsarin mulkin demokuradiyyar da aka ara daga ƙasashen yamma bai yi wa ƙasashen Afirka rana ba.
Tsohon shugaban Najeriyar ya soki tsarin yana cewa cewa ba ya la'akari da tarihin al'ummar Afirka da matsalolinsu, don haka akwai bukatar a maye shi da wani tsari na musamman.
Wasu dai na ganin cewa bai kamata ya kushe tsarin ba, kasancewar shi ne ya yi uwa da makarbiya wajen mayar da Najeriya kan turbar demokuradiyyar a shekarun baya.
Cif Olusegun Obansanjo wanda ya yi furucin a wani taron tattaunawa a kan dimokuraɗiyya a birnin Abeokuta ya ce tsarin dimokuraɗiyyar da aka ara daga ƙasashen yama musamman ma Amurka , tsari ne da ya yi hannun riga da matsalolin al'ummar Afrika saboda ba ya la'akari da tarihin nahiyar da kuma matsalolin al'umominta.
Don haka ne tsohon shugaban ya ce ya kamata al'umomin nahiyar su yi karatun ta natsu, su kirkiri wani tsarin mulki da zai dace da nahiyar.
Sai dai ga alama wannan furucin bai yi wa wasu dadi ba, ciki kuma har da mahukuta a Najeriya.
'Babu abin ɗauka a kalaman Obasanjo'
Fadar shugaban kasa ta ce babu wani abun dauka a cikin maganar Cif Olusegun Obasanjo saboda, a cewarta abinda ya ke so ne kaɗai ke burge shi.
Maitaimakawa shugaban Najeriya a harkokin yaɗa labarai Abdulaziz Abdulaziz, ya ce maganar Obasanjo ba maganar karba ba ce a yanzu.
Ya ce; "Kowa ya san cewa Obasanjo duk da cewa ya yi alkaurin ya daina siyasa amma wannan zaɓe da aka yi na 2023 ya fito ya nuna ɗan takarar da yake yi, ya nuna jam'iyyar da ya ke goyon baya.
Don haka mutumin da ke da jam'iyya yana da ɗan takara kuma aka kada ɗan takararar na shi. Duk wata magana da zai yi a kan shuaabancin da ake kai ba za a karbe shi a matsayin abinda za a dora a sikelin adalci ba.
Sai dai wasu masana siyasa a Najeriyar na ganin cewa akwai fa kamshin gaskiya a cikin maganar tsohon shugaban kasar, sai dai kuma a cewarsu ba shi ne ya kamata ya kushe dimokuraɗiyya ba, tunda da shi aka yi uwa da makarbiyya, aka kaɗa aka raya wajan kafa dimokuraɗiyyar a Najeriya.
Sharhin Masana
Malam Kabir Sa'id Sufi masanin siyasa ne a kwalejin share fagen shiga jami’a ta jihar Kano na cewa bai kamata a yanzu Obasanjo ya ke nuna kiɗansa ba dadi ba.
"Ba wai abinda ya faɗa ba ne ba dai-dai ba . Da yake dai shi ne ya faɗa shi ya sa ake mamaki saboda wasu dalilai"
"A lokacin da yake mulkin soja a tsakanin shekarar 1976 zuwa 1979 su suka karɓi shawara da kuma daftarin da ya sa aka koma turbar dimokuraɗiyya irin wanda mu ke kanta a halin yanzu,
"Na biyu ya ci moriyarsa ya yi shugaban kasa shekara 8 kuma ba tare da a wancan lokacin ya ga laifin abin ba ko ya soke shi , shi ne kusan abin mamakin". In ji Malam Kabir.
Masana da dama dai na ganin cewa matsalar shugabanci da ake fama da ita a nahiyar Afrika ba matsalar ce ta tsarin mulki da ƙasashen nahiyar suka ara suka yafa ba, a ganinsu babbar matsalar ita ce cin hanci da rashawa kuma muddin shugabanni da wadanda ake mulka basu sauya hallayensu ba, to da wuya a ga mai kyau.