Real Madrid ta rage tazarar da ke tsakaninta da Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Saura maki huɗu ya rage tsakanin Barcelona mai jan ragamar teburin La Liga a bana da Real Madrid ta biyu mai rike da kofin bara.
Real ɗin ta je ta doke Leganes 3-0 a wasan mako na 14 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya da suka yi ranar Lahadi.
Kylian Mbappe ne ya fara cin ƙwallo saura minti biyu su je hutu, haka suka koma zagaye na biyu Real tana da ɗaya a raga.
Bayan da wasa ya nutsa ne Valverde ya kara na biyu a raga, sannan Jude Bellingham ya zura na uku, saura minti biyar a tashi daga wasan.
Da wannan sakamakon Real Madrid mai kwantan wasa tana ta biyun teburi da maki 30, wadda ta ci karawa tara da canjaras uku aka doke ta wasa daya a kakar nan.
Barcelona ce ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 34, bayan da ta je ta tashi 2-2 ranar Asabar da Celta Vigo.
Ranar Laraba, Real Madrid za ta je Liverpool, domin buga Champions League, sannan ta karɓi bakuncin Getafe a La Liga ranar Lahadi.
Ita kuwa Barcelona, za ta yi wa Stade Brest masauki a gasar zakarun Turai ranar Talata daga nan Las Palmas ta ziyarce ta ranar Asabar 30 ga watan Nuwamba.











