Arnold ya yi watsi da sabunta kwantiragi da Liverpool, Alonso zai bar Leverkusen

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alexander-Arnold
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan bayan Liverpool Trent Alexander-Arnold ya kara watsi da tayin sabunta kwantiraginsa da Liverpool, daidai lokacin da Real Madrid ke matsa lamba kan daukar dan wasan mai shekara 26, idan kwantiraginsa ya kare a kaka mai zuwa. (Relevo - in Spanish)

Ana sa ran West Ham za ta yi tsayin daka domin dauko dan wasan tsakiyar Ghana Mohammed Kudus kan fam miliyan 85, a gefe guda kuma Arsenal da Liverpool suna zawarcin dan wasan mai shekara 25. (Mail - subscription required)

Kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso, zai raba gari da kungiyar ta gasar wasan Bundesliga ta kasar Jamus a karshen kakar nan duk da cewa kwantiraginsa sai shekarar 2026 za ta kare, inda ake tunanin zai koma Real Madrid. (Eurosport Spain - in Spanish)

Barcelona na son dan wasan baya na Sifaniya mai taka leda a Wolve, Hugo Bueno, mai shekara 22, wanda ke zaman aro a kungiyar Feyenoord. (Sport - in Spanish)

Real Madrid ta fara tuntuba kan dauko dan wasan tsakiyan Jamus mai taka leda Bayer Leverkusen, Jonathan Tah. Barcelona, da Bayern Munich da wasu kungiyoyin Premier League ma suna zawarin dan wasan, wanda kwantiragin sa da Leverkusen za ta kare a kakar wasa mai zuwa. (AS - in Spanish)

Alamu sun nuna Nottingham Forest ba ta da aniyar siyar da dan wasan tsakiyan Brazil, Murillo mai shekara 22, a watan Junairu, bayan tayin fam miliyan 40 da Real Madrid ta gabatar a kan dan wasan. (Daily Mail)

Manchester United da Liverpool na zawarcin dan wasan Fulham Antonee Robinson, mai shekara 27, bayan haskawar da tauraronsa ke yi tun farkon kakar bana. Kungiyar na sake nazari kan rabuwa da BaAmurken a watan Junairun badi. (Football Insider)