Dalilan da suka sa kamfanonin jiragen sama ke dogara da hukumar kula da yanayi a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Priya Sippy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Africa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Filayen jiragen sama a Najeriya sun shiga ruɗani bayan da ma'aikatan hukumar kula da yanayi ta ƙasar, (NiMet), suka tsunduma yajin aiki sakamakon rashin biyan albashi.
An samu jinkiri da ma soke tashi wasu jiragen a biranen Lagos da Abuja da Kano.
Ma'aikatan hukumar NiMet sun yi gangami a kan titunan Lagos, riƙe da alluna da ke ɗauke da saƙonni daban-daban, kamar ''babu yanayi ba tashin jirgi; sai dai kasadar tashi''.
Yayin da kamfanin jirage na United Nigeria Airlines ya ce ya samu wata hanyar samun bayanan yanayi, kamfanin jirage na Air Peace ayyana soke ayyuka ya yi a tawon wunin ranar Alhamis.
Daga baya ma'aikatan sun jingine yajin aikin,bayan ministan sufurin jiragen sama na ƙasar, Festus Keyamo ya gana da ƙungiyoyin ma'aikatan na Nimet.
Ga wasu manyan dalilai uku da suka sa hukumar kula da yanayin ke da muhimmanci ga sufurin jiragen sama.
Tsaron lafiya
Yayin da jirage ke iya tashi a yanayi maras kyau, hukumar kula da yanayi kan ankarar da matuƙan jirage kan duk wata illa da munin yanayin zai haifar, kamar tsawa da walkiya da gajimare da zubar ƙanƙara da ƙarancin gani samakon yanayin hazo.
Jijjigar jirgi wani abu ne da aka saba ji wasu lokuta, to sai dai tsawa na daga cikin abubuwan da ke tsananta shi, lamarin da ke sanya tsaron fasinjojin cikin hatsari.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yayin da ake ganin da wuya jijjiga ta faɗo da jirgi, amma yakan iya haddasa wa fasinjoji munanan raunuka a wasu lokuta har ma da ma mutuwa.
Hasashen yanayin ka iya gano wuraren da za a iya samun jijjiga , wanda ke samuwa idan aka samu sauye-sauye a gudun iska da inda take tunkara.
Matuƙa jirgi kan yi amfani da bayanan yanayi domin kauce wa wuraren da za a iya samun jijjigar jirgin domin rage haɗarin soke tashin jirage.
A Najeriya, mamakon ruwan sama da tsawa abubuwa ne da ake iya samu a kowane lokaci, lamarin da ya sa bayanan yanayi ke da matuƙar muhimmanci ga zirga-zirgar jirage.
"A duk lokacin da aka samu yawaitar tsawa, hakan ka iya haifar da hatsari,'' a cewar George Delanjian, wani ƙwararre a harkar sufurin jiragen sama da ke zaune a Amurka.
"Walƙiya kan iya taɓa jirgi, lamarin da ka iya haifar wa jirgi mummunan jijjiga. A mafi yawan lokuta masu hasashen yanayi sun an wurare da lokutan da za a iya samun tsawa.''
Bayan yanayi na da matuƙar muhimmanci ga tsaron lafiyar jirage, a daidai lokacin da bincike ke nuna samun ƙaruwar jijjiga a jirage, sakamakon batun sauyin yanayi.

Isa a kan lokaci da sanin inda za a sauka
Bayanan yanayi na da matuƙar muhimmanci ga matuƙar jiragen da ke shirin tashi sama.
Yanayin zafi ko sanyi da iska ko ruwan sama kan shafi tafiyar jirgi a sararin samaniya, da kuma yadda zai isa inda ya nufa da wadataccen mai.
Bayanai dangane da guguwa ko iska mai ƙarfi, kan taimaka wa jirgi wajen isa inda ya nufa a kan lokaci.
Shirin tashin jirgi ya ƙunshi tanadin zaɓin wasu filayen jiragen, idan an samu matsala ko an samu sauyin yanayi a wurin da ya yi niyyar sauka.
"Hukumomin kula da yanayi kan bayar da bayanai ga filin ijrgi domin sanarwa cikin kowace sa'a dangane da halin yanayin da filin jirgin ko garin ke ciki, wanda kuma da shi za a riƙa hasashen yanayin wannan rana,'' a cewar Simon King, wakilin hasashen yanayi na BBC.
"Kowane matuƙin jirgi na da waɗannan tsare-tsare a zuciyarsa kafin ya tashi, alal misali idan babu yanayi mai kyau a filin da zai sauka, to dole ya san halin da wasu filayen jiragen ke ciki domin karkatar da jirgin zuwa can, sannan kuma dole ne ya tabbatar yana da wadataccen man da zai kai shi can ɗin.''
Don haka rahoton yanayi ba kawai don kariyar fasinjoji ba ne, yana taimaka wa jirage rage ɓata lokaci da taƙaita mai da rage kashe kuɗi.
Ayyukan da ake yi a filin jirgi
Bayanan yanayi na da matuƙar muhimmanci a cikin farfajiyar filin jirgi kamar yadda yake ga matuƙin jirgi a sararin samaniya.
Hukumomin kula da yanayi kan bayar da bayanai da filayen jirage game da halin da yanayin da ya tunkaro filin jirgin musamman idan zai shafi ganin hanyar jirgi, domin tashi da sauka lafiya.
Matuƙan jirgi, musamman kan duba bayanan hasashen yanayi domin gane gudun iska da inda take tunkata domin samun damar zaɓen hanyar da zai sauke jirginsa.
Haka kuma bayanan yanayi za su taimaka wajen ɗaukar matakin share dusar ƙanƙara a jikin jirgi, musamman ga ƙasashen da ake samun zubar dusar ƙanƙara da kuma ƙara wa jirgi mai mai ko loda masa kaya da saukewa.
"Idan akwai tsawa, ba a ƙara wa jirgi man fetur, musamman saboda walkiyar da ke samu,'' in ji kin King.











