Zakuna da saukar ƙurar Sahara kan birnin Athens cikin hotunan Afirka

.

Asalin hoton, Angelos Tzortzinis/AFP

Bayanan hoto, Ranar Talata ƙura daga yankin Sahara ta sauka a Athens babban birnin ƙasar Girka.
An wallafa
.

Asalin hoton, Dan Kitwood/Getty Images

Bayanan hoto, Hoton wata uwa ɗauke ɗanta a birnin Adre dake ƙasar Chadi bayan sun tserewa rikicin Sudan.
.

Asalin hoton, Issifou Djibo/EPA

Bayanan hoto, A birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar masu zanga-zanga a kan doki, yayin kiran ficewa sojojin Amurka daga ƙasar.
.

Asalin hoton, Issifou Djibo/EPA

Bayanan hoto, Wani mutum riƙe da wani allo ɗauke da saƙo a lokacin zanga-zangar Nijar.
.

Asalin hoton, Ernest Ankomah/Getty Images

Bayanan hoto, Dan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar adawa a Ghana John Mahama ya gayyaci masu riƙe da sarautun gargajiya a Accra babban birnin ƙasar, don sanar da tsohuwar ministar Ilimi Jane Naana Opoku-Agyemang a matsayin mataimakiyarsa a zaɓen da za a gudanar a watan Disamba.
.

Asalin hoton, John Muchucha/Reuters

Bayanan hoto, ƙwararren ɗan wasan motsa jiki Mo Farah na ɗaukar hoto da wata yarinya lokacin ƙaddamar da ɗakin karatu a kimiyyance a Nairobi babban birnin ƙasar Kenya a ranar Lahadi.
.

Asalin hoton, Luc Gnago/Reuters

Bayanan hoto, Yan rawa na cashewa a dandalin al'adu na Abidjan ranar Asabar a ƙasar Ivory Coast.
.

Asalin hoton, Abdullah Doma/AFP

Bayanan hoto, Matafiya cikin motoci run ratsa ta iska mai ƙarfi a binnin Benghazi da ke Gabashin Libya.
.

Asalin hoton, Monicah Mwangi/Reuters

Bayanan hoto, Zakuna a gidan ajiyar dabbobi na Maasai Mara da ke ƙasar Kenya ranar Juma'a.