Gerard Pique na Barcelona zai yi ritaya a ranar Asabar

Gerard Pique ya lashe kofin duniya da wasu kofina 30

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gerard Pique ya lashe kofin duniya da wasu kofina 30
An wallafa

Dan wasan bayan Barcelona Gerard Pique yace ya shirya tsaf domin yin ritaya daga kwallon kafa a wasan karshen da zai bug ana karshe a filin wasan na Nou Camp a ranar Asabar.

Dan wasan mai shekara 35, wanda ya taso a kungiyar ta Barcelona ya shafe shekara hudu a Manchester United, ya yi wannan sanarwar a wani biiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Barcelona za ta yi wasa da Almeria a La Liga ranar Asabar wanda zai zama wasan karshe ga Pique.

“Na sha fada cewa bayan na bar Barcelona babu inda zan iya komawa, kuma haka ne zai faru,” in ji shi.

Pique ya taso a Bracelona ne tun yana yaro a 2004, lokacin da ya sanya hannu kan yarjejeniya da Manchester United.

Dan wasan da ba ko da yaushe yake buga wasa ba a lokacin da yake United wadda ta ci Premier da Champions a 2007-2008, sannan ya kara komawa bangaren Catalonia a 2008.

Yayin da yake bugawa Barcelona ya buga wasa sama da 600 ya ci kofi 30, ciki har da La Liga takwas, da Champions uku da kuma Copa del Rey bakwai.

Na kori Barcelona daga Champions Lig a wannan kakar, kuma itace ta biyu a La Liga maki Daya a bayan Real Madrid da ke matsayi na daya.

A 2018, Pique ya ajiye takalmansa daga bugawa Spain wasa, bayan samun nasara a wasa 102 kuma suka lashe Euro a 2012 da Kofin Duniya a 2010.