Man United na neman Osimhen da Zubimendi, City na zawarcin Trincao

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 26, daga Napoli, waɗanda ke nazarin ko za su iya samun ɗan wasan gaban Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 22, a wani ɓangare na yarjejeniyar. (Calciomercato)
Manchester United na zawarcin ɗan wasan Real Sociedad dan ƙasar Sifaniya Martin Zubimendi, mai shekara 26. (GiveMeSport)
Manchester City da Manchester United suna sa ido kan ɗan wasan gaban Portugal Francisco Trincao, ko da yake Sporting na fatan ƙulla sabon kwantaragi da ɗan wasan mai shekaru 25. (A Bola)
Everton na son ɗaukar ɗan wasan Brazil Luis Henrique, mai shekara 23, daga Marseille a wannan bazarar amma za ta fuskanci hamayya daga Newcastle da Nottingham Forest. (Football Insider)
West Ham na sha'awar sayen ɗan wasan bayan Genoa da Belgium Koni de Winter, mai shekara 22. (Nicolo Schira)
Tottenham da Brighton na cikin jerin ƙungiyoyin da ke sha'awar sayen ɗan wasan bayan Romania Andrei Ratiu, mai shekara 26, daga Rayo Vallecano. (Mundo Deportivo)
Liverpool na sa ido kan ɗan wasan bayan Denmark Anton Gaaei, mai shekara 22, da ɗan wasan gaban Belgium Mika Godts, mai shekara 19, da kuma abokin wasansu na Ajax, ɗan wasan baya na Netherlands Jorrel Hato mai shekara 18. (TBR Football)
Tottenham ba ta da niyyar amfani da zaɓin da ta ke da shi na ɗaukar ɗan wasan gaban Jamus Timo Werner mai shekara 28, kan kwantiragin dindindin a farashin fam miliyan 8.5, bayan ya kammala zaman aron da ya ke yi daga RB Leipzig. (Mirror)
Newcastle za ta amince da tayin fam miliyan 10-15 kan golan Ingila Nick Pope, mai shekara 32, kuma tana sha'awar maye gurbinsa da golan Burnley ɗan Ingila James Trafford, mai shekara 22. (Football Insider)
Barcelona na neman tsawaita kwantiragin ɗan wasan Brazil Raphinha, mai shekara 28. (Mundo Deportivo)
Har yanzu Chelsea na ƙoƙarin kammala cinikin ɗan wasan Gremio ɗan ƙasar Brazil Gabriel Mec mai shekara 16. (TBR Football)











