Hukuncin Kotun Ƙolin Najeriya bai razana APC ba - Gwarzo

Asalin hoton, FACEBOOK/APC
Bayan yanke hukuncin ƙarshe da Kotun ƙolin Najeriya ta yi, wanda ya tabbatar da kujerun gwamnonin jahohin adawa na Kano da Zamfara da Filato da Bauchi, jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar ta ce hakan bai razana ta ba.
Jami'yyar ta ce akwai rata mai nisa tsakaninta da sauran jam'iyyun adawa kasancewar yawan jihohin da take da su, duk da ana ganin nasarorin da jam’yyun adawar suka samu a kotun koli ta kara masu karfi.
A wata hirar da ya yi da BBC wani jigon jam'iyyar ta APC kuma , karamin ministan gidaje da raya birane Injiniya Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce duk wani gunagunin da ake yi lokaci ne zai tabbatar da asalin yadda lamura suke da kuma irin ƙarfin da jam'iyyar take da shi a siyasance.
Ministan ya ce duk maganganun da ake ta yaɗawa game da jam'iyyar gabannin yanke hukuncin kotun duk labarai ne na ƙanzon-kurege, kuma asalin bayanai za su bayyana nan gaba.
'Ana cewa mun rasa Jihohi, ai ba rasa su muka yi ba, harka ce ta kotu, abin da kotu ta zo da shi, mu ma mun shiga kuma an shigar da mu, saboda haka mun yi nasara a wasu kuma a wasu mun yi rashin nasara. Yanzu APC muna da jiha 20 mai bi mana PDP tana da 13, APGA na da ɗaya Labour na da ɗaya, NNPP na da ɗaya, to me za mu ƙyasa a ciki? Jn ji shi.
Ministan ya ƙara da cewa yanzu babu abin da jam,iyyar ke buƙata sai dai zaman lafiya da haɗn kai domin ta cimma manufofinta.
Ya ce 'Shugaban ƙasa ya zo da munufarsa ta raya ƙasa, kuma mafi yawan abubuwan da suka shafi Najeriya idan Allah Ya yarda an yi maganinsu, da wanda suka shafi tsaro da wanda suka shafi raya ƙasa, da karatu da harkar noma da harkokin sufurin jiragen ƙasa'.
Ya yi bayanin cewa akwai dangantakar siyasa mai zurfi tsakanin 'yan jami'iyyar APC da na sauran jam'iyyu kuma babu ta yadda siyasa ba ta kasancewa saboda haka dole ne mutane su ksance masu haƙuri da yanayin da suka sami kansu a fagen siyasa, kuma jam'iyyarsu ba ta fargabar duk wata haɗaka da ake raɗe-raɗin cewa jam'iyyun adawa na iya yi.
Ministan ya ce 'Mu 'yan siyasa ne kuma zaɓe ya gaji cewa wani ya ci kuma wani zai faɗi, idan abu ya kasace irin haka sai mu koma abin da Bature ke cewa 'drawing board' mu ga mene ne ya kawo aka samu matsala, domin idan aka yi haka nan gaba sai a gyara.'









