Ingila ta fitar da tawagar da za ta wakilce ta a World Cup

Gareth na son kai Ingila wani matsayi da a baya ta jima ba ta kai ba

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Gareth na son kai Ingila wani matsayi da a baya ta jima ba ta kai ba
An wallafa

Kocin Ingla Gareth Southgate ya fitar da sunayen 'yan wasan da za su wakilci kasar a gasar Kofin Duniya da za a fara nan da kwanaki a Qatar.

Southgate wanda ya bi sahun takwarorinsa na sauran kasashe, ya fuskanci kalubale wajen zabar yan wasan tawagar gabanin bayyanasu.

Ingla na daya daga cikin kasashen da suke da matasan 'yan wasa da suke taka leda a manyan kungiyoyin da suka yi fice.

Daga baya kocin na Ingila ya dauki masu tsaron raga uku da suka hada da Jordan Pickford na Everton da Nick Pope daga Newcastle sai kuma Aaron Ramsdale na Arsenal da ke matsayi na daya a Premeir.

Masu tsaron baya kuwa akwai Harry Maguire da Luke Shaw duka daga Manchester United, sai Eric Dier na Tottenham, John Stones da Kyle Walker daga Manchester City.

Akwai kuma Kieran Trippier daga Newcastle da Conor Coady na Everton, Ben White na Arsenal, sai kuma Trent Alexander-Arnold daga Liverpool.

'Yan wasan tsakiya sun hada da Jude Bellingham na Borussia Dortmund a Jamus, akwai Mason Mount da Conor Gallagher da suke taka leda a Chelsea.

Sannan Declan Rice na West Ham, sai Jordan Henderson Liverpool, Kalvin Phillips na Manchester City.

Akwai 'yan wasa da dama da aka yi tsammanin sunayensu za su fito cikin wannan tawaga amma ba su fito ba.

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Akwai 'yan wasa da dama da aka yi tsammanin sunayensu za su fito cikin wannan tawaga amma ba su fito ba.

A gaba Gareth Southgate ya kira James Maddison daga Leicester, Phil Foden da Jack Grealish daga Manchester City daHarry Kane na Tottenham.

Akwai Bukayo Saka na Arsenal, da Raheem Sterling Chelsea, Callum Wilson daga Newcastle, sai kuma Marcus Rashford daga Manchester United.

Akwai 'yan wasa da dama da aka yi tsammanin sunayensu za su fito cikin wannan tawaga amma ba su fito ba.

Dan wasan baya na tsakiya Fikayo Tomori na AC Milan da Jadon Sancho na Manchester United da Ivan Toney na Brentford da kuma Jarrod Bowen na West Ham dukansu ba su samu kira ba zuwa gasar.

Ingila da ke rukunin B za ta fara wasanta na farko ne a ranar 21 ga watan Nuwamba, ina za ta fafata da Iran.