Ten Hag zai ci gaba da horar da Man United

Asalin hoton, Getty Images
Erik ten Hag zai ci gaba da horar da Manchester United, bayan da mahukuntan kungiyar suka yi bitar kwazonsa a kakar da aka kammala.
An kuma fuskanci cewar United na tattaunawa kan tsawaita kwantiragin kociyan a Old Trafford, wanda zai shiga kaka ta kare a yarjejeniyar da suka kulla a baya.
United ta fara auna kwazon Ten Hag kan yadda ya gudanar da jan ragamar kungiyiyar daga bayan da ya lashe FA Cup.
Ten Hag, wanda ya fuskanci kalubale da yawa a United, ya yi nasarar lashe FA Cup, bayan cin Manchester City 2-1 a Wembley.
Tun farko an alakanta United da cewar za ta dauki Thomas Tuchel, domin maye gurbin Ten Hag, idan an yanke shawarar korar shi.
Tuchel tsohon kociyan Chelsea da Borussia Dortmund da kuma Paris St German ya ce baya cikin masu neman aikin jan ragamar United.
Dan kasar Jamus ya raba gari da Bayern Munich a karshen kakar da aka kammala, bayan da suka kulla yarjejeniyar kowa ya kama gabansa.
Sauran kociyan da aka alakanta za su iya maye gurbin Ten Hag har da Mauricio Pochettino, wanda Chelsea ta kora da tsohon kociyan Brighton da Chelsea, Graham Potter.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sauran sun hada da na Brentford, Thomas Frank da kuma Roberto de Zerbi da mai jan ragamar tawagar Ingila, Gareth Southgate.
United ta kare a mataki na takwas a teburin Premier League da aka kare, gurbin kasa kwazo tun bayan da aka sauya fasalin gasar.
Koda yake United ta yi fama da yan wasa da suka yi ta jinya, hakan ya sa Ten Hag ya dogara da cewar dalilin da kungiyar ta ci karo da koma baya kenan.
Dan kasar Netherlands ya karbi aiki a Old Trafford kan fara kakar 2022, kuma shi ne kociyan United na biyar tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya a 2013.
Sauran da kungiyar ta dauka sun hada da David Moyes da Louis van Gaal da Jose Mourinho da kuma Ole Gunnar Solskjaer.
Ya koma Old Trafford bayan kammala kaka hudu da rabi a Ajax, inda ya lashe Eredivisie uku da Dutch Cups biyu.
A kakar farko da ya ja ragamar United ya kare a mataki na uku a Premier League da daukar League Cup da kai wa wasan karshe a FA Cup.
Ya dauki kofin farko a United cikin watan Fabrairun 2023, bayan cin Newcastle United ya dauki Carabao Cup, amma Manchester City ta doke su a wasan karshe a FA Cup da cin 2-1.
Ya fuskanci kalubale a kakar 2023/24, ciki har da fitar da United daga Champions League a karawar cikin rukuni, wadda ta yi ta karshe a rukunin farko.
United ta yi rashin nasara shida a wasa 10 har da wanda Galatasaray da Bayern Munich suka doke ta a Champions League.
Haka kuma United ta kare a mataki na takwas a teburin Premier League, gurbin da ya cikin wadanda za su wakilci Ingila a gasar zakarun Turai a badi.
Sai dai daukar FA Cup da ta yi ya sa za ta kara a Europa League a kakar da za a shiga.











